Hukumar kula da yan gudun hijira ta duniya ta samarma sama da Mutane 3000 matsuguni

0
422

Hukumar kula da yan gudun hijira ta duniya ta samarma sama da Mutane 3000 matsuguni

Daga Zubairu T M Lawal Lafia

Hukumar kula da yan gudun hijira ta duniya tace ta samarma dubam yan gudun hijirar da sukantsero daga yankin qasar Kamaru muhalli. Hukumar tace ta samu hadin giwa da Gwamnatin jihar Cross-River dake tarayyan Nijeriya. Idana aka samar da matsugunansu a kuayen Agadon dake qaramar hukumar Agoja cikin jihar Cross-River .
Gwamnatin Jihar ta taimaka da fili mai fadin helta 52 ta yadda za’asamar da matsugunai irin wanan.
Ko a shekarun 2017 hukumar kula da yan gudun hijira ta maida dubbanni yan gudun hijira zuwa gidajensu na sali . sanan wadanda gidajen nasu keda matsalolin da zai hanasu komawa tuni ta samar masu da matsugunan a wasu yankuna da zai dace da zamantakewarsu.
Takara da cewa cikin guraren da aka samu domin tsugunar da wadanda suke tserowa daga kan iyakan qasar Kamaru sun hada da yankin Cross-River da Taraba da Akwa-Ibom da jihar Benuwe .
Hukumar takara da cewa yanzu haka tanada sunayen yan gudun hijira samada mutum 21,291 dake hannunta akasarinsu yarane da mata . ya zama dole a samar masu da matsugunai da bude hanyoyi da wajen ansar magani domin kula da kiwon Lafiya da ruwansha mai tsafta da makarantu saboda suma rayuwarsu ta yi daidai da sauran yara .
Yin hakan shine zai kwantar masu da hankali.
Haka zalika masu hannu da shuni suna kai dauki domin taimakawa rayuwan yan gudun hijirar . Kungiyar qasashen Turai wato EU tai bada nata tallafin ta yadda akayi nasarar maida wasu yan gudun hijirar Jihar Benuwe kauyukansu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here