Tauraron Da Ke Yakar Ta’addanci Ba Tare Da Makami Ba.
Imrana Alhaji Buba Hazikin Matashi ne da ya kammala digirin sa na farko a fannin kimiyar Siyasa da daraja ta farko.
Imrana ya kasance shugaban kungiyar Yaki da Ta’addanci, wanda ya kasance ya na yakar ta’addanci ba tare da amfani da makami ba, ya kasance ya na zagayawa tsakanin kasashe yana gabatar da darasi kan hadarin ta’addanci ga matasa, kasashe da dama suna yaba aikin wannan bawan Allah, amma abin mamaki kasar shi bata san ya na yi ba.
Daya daga cikin nasarorin da ya samu shi ne kyautar matasa ta Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth.
Da a ce Imaran yadda ya kware a fannin ilimin kimiyar siyasa a kwallo ne y ke da wannan kwarewar da yanzu duk duniya an San shi, hotunansa kuma tuni da sun cika kafafen sadarwa na zamani. Shin ta ya za a ayi mu samu cigaba bayan ba mu karfafawa masu iliminmu kwarin guiwa? Kasa tana daukaka ne kawai da fifita masu ilimin cikinta da kuma karfafa masu guiwa.
Babu ko shakka, kasarmu cike take da matasa masu hazaka kamar Imrana, amma saboda ba mu karfafa masu guiwa, sai wasu kasashe su dauke su su yi amfani da su domin cimma nasara a kasarsu.
Imrana ya na aiki ne kasa rika domin Samar da zaman lafiya da dorewarsa, muna alfahari da kasancewarsa Dan Nijeriya kamar yadda Sarauniyar Ingila ta tambaye shi akan ko shi dan Arewacin Nijeriya ne?
Muna fatan a rika karfafawa matasa guiwa domin mu yi alfahari da su a kasar mu.