WANE BINCIKE EFCC KEYI A JAHAR KATSINA?

1

WANE BINCIKE EFCC KEYI A JAHAR KATSINA 

Daga wakilanmu

Wani labari da jaridar Taskar labarai ta dau tsawon lokaci tana bibiya..shine na binciken da hukumar EFCC keyi a Bangaren dake kula da karatun manyan makarantu na jahar katsina.( Department of higher education) Wanda ada kwamishinan ilmi na yanzu .. farfesa Badamasi Lawal charancii ke Mai ba gwamna shawara a wajen ..yanzu kuma Malam Bishir Ruwan godiya ke Mai baiwa” .gwamna shawara a wajen.
Tun kwanakin baya .. Taskar labarai ta samu tabbacin cewa.. hukumar EFCC sunyi awon gaba da manyan Jami an bangaren.. wadanda suke da alaka da kudi..kuma har an tsare su …tsawon lokaci a Abuja kafin daga bisani a bayar dasu beli
Wata majiya a hukumar ta EFCC ta tabbatar wa da TASKAR LABARAI cewa ana wani bincike .a sashen kuma an gayyaci duk Wadanda abin ya shafa Inda suka amsa gayyatar Bayan yi masu tambayoyi..da rubuta bayanansu..an bayar dasu beli.
Majiyarmu ta tabbatar cewa..wadanda aka gayyatar sun dau kwanaki a tsare.kafin su samu beli..
Binciken ya tabbatar Mana cewa ..zargin nada alaka da kudin karo karatu na wasu dalibai dake karatu a kasashen waje.. Yan jahar Katsina…Wanda gwamnatin Katsina ta bayar Don a biya makarantun da daliban Katsina ke karatu..Mai makon da amsar kudin a biya makarantun da abin ya shafa sai kawai aka zuba su cikin wani asusun ajiya. Wanda bai Shafi ..ma aikatar ba..bai kuma alaka da makarantar da za a biya..
Binciken da mukayi ya gano kudaden suna da yawan gaske Don miliyoyi masu tarin yawa.ne . binciken mu ya gano cewa.. lamarin ya faru ne a zamanin da tsohon Mai ba gwamna shawara Wanda yanzu kuma shine kwamishinan ilmi Yana rike da wurin.
Binciken mu ..sun gano cewa ..wani daga cikin ma aikatan , ma aikatar ya tseguntawa hukumar EFCC..a tsarin na in ka bayyana sirri za a baka wani Kashi na abinda da aka gano. Nan da nan sai hukumar ta EFCC ta fara aikin ta..
Binciken mu..ya jiwo Daya daga …cikin wadanda ake zargi na bayyana cewa ..sunyi abinda sukayi ne bada wata manufar sace kudin ba..
Sai Domin Adana kudaden kafin lokacin da zasu turawa makarantun yayi…da niyyar da lokaci yazo sai su cire su tura.
Taskar labarai tayi kokarin Jin ta bakin hukumar ta ilmin manyan .. makarantun abin yaci tura ..Jami in hudda da jama a na sashen yace ..baida wata masaniya ..Akan lamarin sai dai a rubuto..da aka rubuto ..kuma sai akace takardar ta bace…ba a San Inda aka Kai ta ba.

1 COMMENT

  1. Wannan abin kunya had INA ? Kwamisina da ke cewa zai kawo gyara a maaikatar Ilimi ta jihar Katsina yau ace ana zargin shi da sama da fadi ? Wannan 6atanci ne ga Gwannatin mai Girma Dallatun Katsina !

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here