AISHA JUMMAI ALASAN TA SHA DA KYAR YAYIN DA AKA YI YUNKURIN HALLAKA TA.

0

Kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa, ‘yar takarar gwamnan jahar Taraba Aisha Jummai Alhassan, wacce aka fi sani da Mama Taraba ta sha da kyar yayin da aka yi yunkurim hallaka ta. Wannan al’amari ya faru ne a yayin gudanar da zaben maye gurbi a jahar.

Maman Taraba, tsohuwar ministar Najeriya ce a kan harkokin mata. Wadda Buhari ya naɗa ta yayin da ya haye gadon shugabancin kasar nan a shekara ta 2015. Amma ta yi murabus ne ranar 27 ga watan Yulin shekarar da muke ciki.

A kwanan nan ta bayyana muradinta na fitowa takarar gwamnan jahar Taraba. Abinda ya sa ta zama zakaran gwajin dafi don kasancewarta mace ta farko da ta taɓa bijirowa da irin wannan kudiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here