An Nada Mataimakin Gwamna Sarauta Kafisu a Nasarawa

0

An Nada Mataimakin Gwamna Sarauta Kafisu a Nasarawa

Daga Zubairu Muhammad

Masarautar Karshin dake yankin Raya qasa na Karshi a Qaramar hukumar Karu dake Jihar Nasarawa ta nada Mataimakin Gwamnan Jihar Mister Silas Ali Agara a matsayin Sarautar Kafisu na Karshin .

Nadin Sarautar da ya gudana a ranar Laraba a fadar Sarkin Karshin Alhaji Ahmad Abdullahi Hasan. Wanda akewa Laqabi da (Yankanajeh)dake garin karshin. Shi ya tabbatar da wanan nadin da kansa a Lokacin da Mataimakin Gwamna Hon.Silas Ali Agara yaje gaisuwar Sallah a Fadar nasa ,dake Qaramar hukumar Karu a ranar Laraban qashe garin Sallah.

Masarautar tace; ta duba cancantarsa a matsayinsa na mutumin dake da daraja na biyu a Jihar Nasarawa amma bai dauki kansa a bakin komaiba yana biyayya ga mutani yadda ya kamata.
Kuma yana tafiyar da aikinsa bisa turbar gaskiya da rikon Amana tsakaninsa da maigidansa dama dukkanin alumman Jihar.

See also  FG realised N174b from 2020 marginal field bid round, says Komolafe

Tace; saboda haka wanan shine sakayyar goron Sallar da zamu baka kamar yadda muka tabbatar baka da nauyin kafa muka nada maka wanan Sarauta na cancanta mai suna Kafisu.

Da yake maida Jawabi ta bakin Jami’in Yada Labaransa Godspower Ede.Mataimakin Gwamna Hon.Silas Ali Agara yayi dubun godiya da samun wanan mukamin da bai taba yin mafarkin zai sameshi a irin wanan lokacin ba.
Mataimakin Gwamna yace; “abinda bamuyi tsammaniba sai gashi mun sameshi saboda munzo gaisuwar Sallah ne kamar yadda muka saba duk Shekara, sai gashi Ubanmu Mai Martaba Sakrkin Karshin ya nada mini wanan Sarauta wanda kuma zanyi alfahari da ita komai Daren dadewa bazan manta da wanan ranarba”.

Ya kuma mika dubun godiya ga Masarautar Karshin da alumman yankin Raya Qasa ta Karshin da alumman Jihar Nasarawa baki daya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here