CIN ZARAFIN YARA KANANA DA TAKE HAKKIN BIL’ADAMA A GIDAN SOJA

0
653

Wata mata soja mai suna Esther Ozoekwu daga jihar Ebonyi tana zaune a barikin sojoji mai dauke da adireshi kamar haka CDQ 14 FLAT 12 IKEJA CONTENTMENT ARMY BARRACK tana da wata karamar yarinya ‘yar aikin gida mai suna Nkiruka kuma tana matukar cim zarafin yarinyar

Idan kuka kalli wannan hoton zakuga yadda sojan tayiwa wannan yarinya Nkiruka dukan tsiya ta farfasa mata jiki saboda wai yarinyar bata wanke kwanukan abinci akan lokaci ba, ankai karar sojan gurin manyanta a cikin barikin sojoji amma basu dauki wani mataki ba

Don haka aka yanke shawaran sanar da duniya domin a ceto wannan yarinya daga hannun azzalumar soja sannan a mayar da yarinyar gaban iyayenta ita kuma sojan a tabbatar an hukuntata bisa doka

Dr. Idris Ahmed
CUPS,
19-8-2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here