SAKON BABBAR SALLAH: Matawallen Maradun Ya Shawarci Al’ummar Zamfara Su Zauna Lafiya

0
845

Mai takaran gwamna a karkashin tutar jam’iyyar PDP, Rt. Hon. Dakta Bello Muhammad (Matawallen Maradun), a cikin sako na musamman na babbar sallah ga al’ummar Jihar Zamfara, ya yi kira a gare su da su ci gaba da zama lafiya da juna, musamman ganin yadda aka gudanar da shagulgulan Sallah babba.

Dakta Bello ya taya Gwamnan Jihar Abduaziz Yari Abubakar da Masarautun jihar bisa murnar gudanar da shagulgulan Sallah, inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a yi amfani da lokutan Sallah da ake gabatar da hadaya domin samun albarka bisa kyawawan ibadun da addinin Musulunci ya shimfida.

Ya kara da cewa, “A daidai wannan lokaci da ake gudanar da shagulgulan babbar Sallah, ina taya daukacin al’ummar Zamfara murnar wannan babbar rana, kuma zan yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’umma da su guji dukkanin abin da zai haddasa rashin zaman lafiya, kuma su guji tayar da fitintinu da zai haddasa rasa rayuka da dukiyoyin al’umma. Hakan zai tafi daidai da tsarin da ya kamata al’umma su koya daga babbar Sallah,” in ji shi.

“A kan haka ne, na ke kara kira ga gwamnati da ta sani hakkinta ne ta tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’umma, musamman a yadda Jihar Zamfara take ciki, don haka ya zama wajibi gwamnati ta fito kai da fata ta tabbatar ta dauki aikinta gadan-gadan,” cewar Matawallen Maradun.

Dan takaran ya ce hakan na daga cikin muradunsa inda Allah Ya ba shi damar yin nasara, inda ya ce daya daga cikin manyan muradunsa, sun hada da tabbatar da wanzar da zaman lafiya a fadin Jihar Zamfara.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da sada sakonnin zaman lafiya da fahimtar zuwa a tsakaninsu a lokutan Sallah da bayan lokutan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here