TA SAYAR DA BUDURCINTA AKAN KUDI NAIRA MILIYAN DARI DA HAMSIN

0

Wata Bajamusa mai shekara 36 ta tallata budurcinta a shafin yanar gizo a kan kudi €250,000. Ta nuna cewa kodayake shekarunta sun yi nisa, amma kuma budurcinta shi ne mafi muhimmanci. Mandy mai shekara 36 ta shelanta gwanjon budurcin nata ne a shafin yanar gizo na “Cinderalla Escorts”. Wanda ya yi nasarar wannan ciniki, wani hamshakin dan kasuwa ne, da ya biya zunzurutun kudi €250,000. Mandy ta shirya haduwa da wannan kasuwa a watan Satumba. Ta bayyana cewa za ta yi amfani da wadannan kudade don taimaka wa mabukata da kuma inganta rayuwarta. Ita dai wannan Bajamusa tana aiki a matsayin mai hidima a cikin jirgin sama, ta yaba wa wannan shafin yanar gizo, da ya taimaka mata wajen tallata kanta a yanar gizo. Ta samu labarin shafin cinderalla escorts ne a wata jarida, inda aka bayyana shi a matsayin wata kafa da manyan ‘yan kasuwa kan sayi abubuwa da dama a birnin Munich. Mandy ta nuna yadda ta kusan yanke tsammanin samun irin namijin da ya dace da ita. Ta shaidawa jaridar FEMAIL, irin kokarin da ta yi wajen kare budurcinta. Domin yin hakan abu ne mai wahala. Nakan lallashi kaina ta hanyar yin amanna da haduwa da namijin da nake buri a kowace shekara. Mandy ta kara jaddada aniyarta wajen amfani da wadannan kudi wajen bunkasa makomarta da tallafa wa danginta, da kuma taimakawa mabukata. Ta kara da cewa duk da yake shekarunta sun fara nisa, hakan ba za ya sa ta karaya ba. Kowace mace tana rasa budurcinta ne sau daya tak, da zaran ta yi sakaci. Amma kuma, idan ta yi hakuri ta jure hakan kan zama abin tikaho da alfahari a gare ta. Shi kuwa wannan dan kasuwa za ya hadu da Mandy ne, a wata mai kamawa don cikasa yarjejeniyar wannan ciniki, kamar yadda ta shaidawa FEMAIL. Ta ci gaba da cewa ” na mayar da hankali na kan aiki na ne, domin ban hadu da irin namijin da ya dace da ni ba, kuma haka abubuwa suke kasancewa a wasu lokuta. Ma’aikaciyar jirgin saman, ta ce har yanzu tana fatan cikar burinta wajen haduwa da irin namijin da take bukata, duk kuwa da sayar da budurcinta da ta yi. “Ban karaya ba, domin wata rana zan iya haduwa da shi, matukar yana so na ba za ya damu da matsayi na na budurwa ba ko akasin haka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here