Yan gudun hijira 65,000 na fama da matsalar Ruwansha a Sansanin Gwaza.

0

Yan gudun hijira 65,000 na fama da matsalar Ruwansha a Sansanin Gwaza.

Daga Zubairu Muhammad

Yan gudun hijiran sun dade suna fuskantar wahalar ruwan sha, tun baya fara rikicin Boko Haram da yakici_yaki_cinyewa, sakamakon yadda ‘yan Boko Haram din suka bi duk rijiyoyen Burtsatsensu suka lalata.

Wanan ya sanya Majalisar Dinkin Duniya da hadin Gwiwar Gwamnatin jihar Barno za su kawo karshen wahalar Ruwan shan da ‘yan gudun hijira suke fama da shi a sansanin su dake kusa da karamar hukumar Gwoza.

Wajen samar da ruwa na Pulka, shi ke samar ma da Mutane wajen 65,000, wadanda suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da kuma kauyakun da ke kewaye da wajen.

‘Ma’aikata dai daga Majalisar Dinkin Duniyar da kuma hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Barnon sun koya ma ‘yan gudun hijiran yadda za su iya haka Rijiyar Burtsatse da kan su.
‘Yan gudun hijiran dai suna samun ruwan amfani ne ta hanyar taran Ruwan sama a wannan lokaci na damina. Sai kuma wani rijiyar Burtsatse mai amfani da hasken rana wanda Gwamnatin Jihar Barno ta gina musu a watan Afurilun da ya gabata.

See also  SHANU 700 ZA A YANKA A BA MABUKATA 4900 A KATSINA

Sannan kuma akwai wasu motocin daukar Ruwa da suke dibo musu ruwa daga garin Gwaza dake kusa da Sansanin ‘yan gudun Hijiran.

Bincike dai ya nuna ko wane Mutum zai iya rayuwa da Litan Ruwa 15 ne a rana. Kuma adadin mutanen dake zama a Sansanin ‘yan gudun hijiran sun kai 65,000, dan kaha suna bukatan ruwan da yakai Lita 975 a ko wace rana, amma kuma ko kusa da hakan basa iya samu.

Akarshe dai an Hukumar bada Agaji ta rarraba musu kayan masarufi, sannan kuma akai musu alkawarin samar musu da isashshen ruwan anfani nan da dan lokaci kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here