Ko Kasan Mutane Goma Da Ake Nema A Duniya Ruwa Jallo?

0

Ko Kasan Mutane Goma Da Ake Nema A Duniya Ruwa Jallo?

Daga Abdulrahman Aliyu

Wannan Duniyar cike take da mutane masu aikata ayyukan ta’addanci kalaka, Ya’allah da sunnan addinai ko kuma akasin haka, wasu kuma sukan kira kansu da masu jihadi, inda suke amfani da wannan damar suna salwantar da rayuka bila’adadin da sunan jihadi.
A duniya akwai mutane goma da mujallar Improb ta wassafa a 2018 a matsayin fittun masu aikata ayyukan ta’addanci da ake nema a duniya ruwa a jallo, kuma an sanya alawajar kudi ga duk wanda ya kawo waxannan mutane ko kuma ya bayar da bayanin yadda za a kama su a raya ko a mace.
Jaridar Taskar Labarai ta bibiyi wannan rahoto na Mujallar Improb domin kawo maku jaddawalin wadannan mutane goma, ta alakari da nauyin ayyukan kowane daga cikinsu.

1. Ayman al-Zawahiri: Ayman shi ne shugaban fitattciyar kungiya jihadi ta al-Qa’ida tun bayan da aka kashe Shugabanta Osama bin Laden a shekarar 2011, kafin zama shugaban qkungiyar shi ne babban kwamandan wanda ke bi ma Bin Laden a cikin kungiyar.
Al-zawahiri dan asalin kasar Egypt ne kuma yana da hannu dumu-dumu a harin da aka kai wa ofishin jakadancin Amerika da ke Nairobi a Kasar Kenya da kuma Dar es Sallam a Tanzaniya, a shekarar 1998 wanda ya haddasa asarar daruruwan rayuka.
A shekarar 2008 sojojin kasar Fakisatan sun bayyana nasara cabke al-Zawahiri a arewa maso yammacin kasar Fakistan.
A Shekarar 2012 ne al-Zawahiri yabayyana cewa a rika kama duk wasu Turawa ana garkuwa da su a kasashen Musulmi, wanda wannan da’awar tasa ta sanya karuwar ayyukan ta’addanci da kuma sanya shakku a zukatan Turawan da ke halartar wadannan kasashe.
Wannan ne yasa aka ayyana shi a matsayin dya dga cikin wadanda gwamatin Amuruka ke nema ruwa a jallo kuma an sanya alawajar dala miliyan ashirin da biyar ($25 million) ga duk wanda ya kama shi ko ya bada bayanin yadda za a kama shi.

2. Dawood Ibrahim: ya na daya daga cikin wadanda ake nema Ruwa a jallo a Duniya, da asalin kasar Indiya ne, wanda ked a akamfanin da ake aikata ayyukan ta’addanci a Indiya, wanda ya kirkira a shekarar 1970 mai suna D-Company, ya zama abun nema tun a shekarr1980, amma bai zama shararren Dan ta’adda da duniya ke nema ba sai a shekarar 2003. Dawood na zaune a Pakistan ne, duk da cewa gwamnatin Pakistan ta karyata zaman sa a kasarta.
Ya na da hannu dumu-dumu a harin tayar da bamabamai da aka kai a shekarar 1993 a Bombay, sannan kuma da hannusa aka tayar da bamabamai goma sha biyu a Mumbai wanda ya haddasa asarar rayuka 257 da kuma sama rauni fiye da mutane 717. Ibrahim Dawood yak ware wajen ayukan ta’addancin sa a kasashe irinsu India da Pakistan United Arab Emirate. Ana neman sa ne ruwa a jallo bisa tuhumomi da dama, wadanda suka hada da kisan kai da safarar miyagun kwayoyi da kumasauran Ayyukan ta’addanci da dama, shima kamar al-Zawahiri na sanya dala miliyan ashirin da biyar ga duk wanda ya kamo shi ko yabayyana yadda za a kama shi.

3. Abu Bakr al-Baghdadi: shi ne shugaban kungiyar ISIS wanda ta rika kai hararen ta ga turawa a shekaru biyu da suka wuce. Al-Bagadadi daya ne daga cikin dakarun kungiyar al-Qa’ida daga shekarar 2006-2013, kafin ya balle ya koma shugaban kungiyar ISIS, ana tuhumar sad a aikata laifuka kalakala wadanda suka hada da garkuwa da mutane da fede ga wata jami’ar kare hakkin bil’adama mai suna Kayla Mueller. Ana tunanin al-Bagadadi yana boye a garin Raqqa a cikin kasar Syria. A wani Rahoto da BBC Hausa suka kawo a ranar 24/8/2018 ya nuna cewa al-Bagadadi ya na nan da ransa bai mutu ba, kuma har ya bayyana aw wani faifan bidiyo yana killace kansa daga tabarbarewarda kungiyar sa ta yi.
Shi ma dai kamar sauran na sanya dala miliyan ashirin da biyar ga duk wanda ya kamo shi ko yabayyana yadda za a kama shi

4. Semion Mogilevich: shi ne shugaban duk wani dan’tadda a Rasha, yana da hannu a manayan ayyukan ta’adaddanci wadanda suka hada da safarar makamai da safarar miyagun kwayoyi da daukar nauyin kasahe-kashe da karuwanci da damfara, kai har ma da safarar makamai masu linzami.
Ana ganin cewa Mogilevich a matsayin mutum mafi hadari a duniya kuma wanda ke da hannu a duk wani kullin siyasa a Rasha, a shekarar 2006 ana ganin cewa akwai kulli mai karfi tsakanin Alexandara Litvinenko da Mogilevich da kuma shugaban kasar Rasha Valdamir Putin. Bayan samun wannan rahoton sai aka samu gawar Litvienko an kasha shit a hanyar shayar da shi guba.
Fitattun sunayen sa sun hada da “Don Semvon da kuma The Brainy Don, an kama shi a shekarar 2008 a Mascow saboda rashin biyan haraji, an sake shi bayan shekar guda. Hukuma FBI ta sanya sunan sa cikin mutane goma da ake nema a Duniya Ruwa a Jallo a 2009 amma an jire sunan sa a shekarar 2015 bayan wata yarjejeniya tsakanin kasar Amerika da Rasha.

See also  'YAN PDP KU YI SHIRIN KO-TA-KWANA

5. Matteo Messina Denaro: Fitattacen Dan ta’adda shugaban duk wani dan ta’adda a Sicilian, ya dare bisa mukamin shugaban kungiyar ta’addanci na duniya bayan mutuwar Bernardo Provenzano da kuma bayan kama Salvatore Riina a 2007 yana daga cikin fitattun yan’ta’adda a Italiya, an kama shi sau ba iyaka. Ana kiransa da sunan Diaboli, ya kasance fitattace a ayyukan ta’addanci wadanda suka hada da safarar miyagun kwayoyi da sauran ayyuka na asha.
A shekarar 1993 ya na da ahannu tsundum a ayyukan ta’addanci na tayar da bamabamai da aka yi a Italy wanda ya haddasa asarar rayukan mutane goma da raunata sama da mutane 93 da sarar dukiya da dama. Tun daga wannan lokacin ba a kara ganin Denaro ba har zuwa yau dinnan d ake nemansa ruwa a jallo.

6.Alimzhan Tokhtakhunov: fitaccen Dan Kasuwa wanda ake zargi da ayyukan ta’addanci a kasar Rasha, an fi sanin sunansa da Taiwanchik, ana zarginsa da ayyukan ta’addancin wadanda syuka hada da sumogal da damfara da kuma haramtattar caca. An taba kama shi a Italy a shekarar 2002 amma an sake shit un kafin a gabatar das hi gaban kotu.
Ya kasance tsohon dan kwallo a kulub din kwarrrau a Rasha, kafin a fara neman sa ruwa jallo bisa ayyukan ta’addanci a duniya.

7. Felicien Kabuga: Daya daga cikin wanda ake nema ruwa jallo a Afirika, kuma fitaccen attajiri sanannen dan Kasuwa a kasar Rwanda, wanda ya samu kudin sat a hanyar noma ganyen shayi a Ruwanda, ana zargin sad a hanu wajen kasha-kashen kabilanci da aka yi a Rwanda. Kabuga ya kasance wanda ya mallake gidan Rediyo da na Talabijin a Rwanda wadanda suika taka muhimmiyar rawa wajen tunzura mutane har k yi kashekasahen karedangi a kasar.bayan wannan kuma ya kawo wa kafilar Hutus makamai wanda aka yi amfani dasu wajen kasha mutane sama da dubu dari biyar zuwa miliya daya a Rawanda, haka kuma yana da hannu wajen murkushe tattalin arzkin kasar.
Wannan ne yasa ake tuhumarsa da laifi kala-kala wanda ya hada da haddasa kisan kare dangi, Kabuga ya gudu tun lokacin da aka kare fadan kare dangi a Rwanda. Ana zargin yana kasar Kenya yana gudanar da kasuwancinsa.

8. Omid Tahvili: An haife shi a Iran, amma ya kasance yana aikata ayyuka ta’addanci a Canada, in da ya jona da sauran fitattun masu ayyukan ta’addanci a duniya. Ya sha arcewa daga kamun da ka yi masa, misali a shekarar 2007 ya arce daga gidan yari bayan da ake zargin ya hada kid a masu tsaronsa inda ya basu toshiyar baki, wanda har yanzu baa san inda yak e ba, shi ysa ka sanya sunansa a jerin mutane goma dake nema a duniya ruwa a jallo. Ana zarginsa ta ayyukan ta’addanci wadanda suka hada da damfara ta yanar gizo da damfara ta kasuwancin yanar gizo da garkuwa da mutane da muzanta mata da fede da sauransu an sanya dala miliyan uku ga duk wanda ya kamo shi ko kuma ya yi sandain kamashi.

9. Ismael Zambada Garcia: shi ne shugaban kungiyoyin ta’addanci a kasar Mexico, inda yake jagoranta wata kungiya mai suna Sinaloa Cartel wadda ta kasance daya daga cikin kwarraun masu safarar miyagun kwayoyi a duniya.
Ana kiransa da sunan El Mayo an ayyana shi dilam kwayoyi a Mexico a shekarar2016 , ya klware wajen shuigar da kwayoyi da kayan maye a a America, wanda ya hada da jirgin sama da kuma na ruwa . an sanya alawajar dala miliyan biyar ga duk wanda ya damko shi ko kuma ya yi hanyar kama shi.

10. Joseph Kony: shi ne shugaban kungiya Lord’s Resistance Army (LRA), wadda ta yi tashe a shekarar 1987 ya ayyana kasan a matsayin annabi, sannan kuma ya nuna cewa yana da aljannu. Ya fara ayyukansa a Ruwanda kafin daga baya ya koma Damakuradiyyar Congo da kuma Kudancin Sudan, ya kware wajen garkuwa da kananan yara ya tilasta masu yin ayyukan ta’addanci ko kuma ya sayar das u a matsayin bayi.
A 2005 Kony ya bayyana a kotun duniya kan ayyukan ta’addanci, kafin daga baya gwamnatin Amerika da ta Kenya su ayyana yin farautar Kony Ruwa a jallo.

Wadannan sune jerin mutane goma da ake nema a duniya ruwa a bisa aikata manayan ayyukan ta’addanci, shin ko ka san wani kuma da ake nema ruwa a jallo bisa irin wadannan ayyukan?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here