TURAKI YA YI FATAN KASANCEWA MAFITA GA AL’UMMAR NAJERIYA

0

TURAKI YA YI FATAN KASANCEWA MAFITA GA AL’UMMAR NAJERIYA

Daga Bishir Suleiman

Ya faɗi haka ne, a cikin wata takardar da daktan yaɗa labaransa, Sole Atere ya sanya wa hannu.

Ɗantakarar Shugabacin ƙasar, a jam’iyyar PDP Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, ya yi kira ga shugabanin da al’ummar Najeriya da su cigaba da miƙa kukan ga mahalicci, don neman mafita da samun rahamar.

Dantakarar, ya miƙa saƙon gaisuwar sallah, ga ɗaukacin Musulman Najeriya, tare da taya su murnar zagoyawar wannan muhimmiyar rana, wadda Allah SWT ya umurci kakanmu Annabi Ibrahim AS da yin layya.

Rana ce mai matuƙar muhimmanci, ga ɗaukacin musulmai wajen kaɗaita Allah tare da neman biyan buƙatocin kai dama na ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga al’umma, da su yi amfani da wannan rana, wajen ƙoƙari samar haɗin kai da ƙara himmatuwa wajen jaddada zaman lafiya da kwaciyar hankali a ƙasar nan.

See also  Gwamnan Ondo ya yabi shirye-shiryen rage raɗaɗin rayuwa

Ya kuma taya murna ga ɗaukacin mahajjatan da suke a ƙasar Saudia domin sauke farali da fatan Allah ya karɓi ibadojin da ake yi.

Ya kuma yi fatan, mahajjantan, za su sa ƙasar nan, a cikin addu’o’insu, dangane da halin ƙuncin da ake ciki.

Kazalika, Ɗantakarar shugabancin ƙasar, ya nuna juyayinsa kan abin bakin cikin da ya same su na mutuwar abin sonsa sakamakon faɗa makiyaye da kuma waɗanda ake kashewa a rikice rikicen ƙasar nan, da fatan Allah ya gafarta masu.

An samu wannan takarda ne a hannun, Sole Atere, Daraktan kafafen sadarwa na zamani da yaɗa labarai, kuma shugaban yaƙin neman zaɓen, ɗantakarar shugabancin ƙasar nan, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, a offishinsa na Abuja

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here