GWAMNATIN KATSINA TARE DA HADIN KAN KUNGIYOYIN DUNIYA MASU BADA TALLAFI ZASU RABA GIDAN SAURO DON RAGE ZAZZABIN CIZON SAURO

0

GWAMNATIN KATSINA TARE DA HADIN KAN KUNGIYOYIN DUNIYA MASU BADA TALLAFI ZASU RABA GIDAN SAURO DON RAGE ZAZZABIN CIZON SAURO

Gwamnatin Tarayya tare da kungiyoyi masu bada tallafi na Duniya sun hada kai da gwamnatin jihar Katsina domin samar da gidan Sauro kyauta ga Al’ummar jihar Katsina a dukkanin kananan Hukumomi 34 na jihar domin yakar cutar zazzabin cizon Sauro(malaria).

Katsina Media and publicity ta samo wannan labarin ne a lokacin da wakilan Gwamnatin Tarayya dana kungiyoyin masu bada tallafi suka kaima Gwamnan jihar Katsina, Rt.Hon.Aminu Bello Masari ziyara a fadar gwamnatin jihar Wanda akafi sani da Muhammadu Buhari House a ranar Alhamis.

Wakilan gwamnatin tarayyar sunzo ne bisa jagorancin Ministan Lafiya Dr.Isaac Adewale. Wakilin nashi yace sunzo Katsina ne domin tattaunawa da Gwamnan kuma suyimai bayani game da kokarin da ake na yakar zazzabin cizon Sauro domin sunzo ne don haka suke son raba Gidan sauro mai dauke da magani Wanda yakai 4,742,765 ga magidanta a fadin jihar.

Ya kaara da cewa gwamnatin jiha itace zata dauki nauyin kudaden da za’a kashe yayin rarraba kayayyakin.

Shugaban kungiyoyin masu bada tallafin ya fadima Gwamnacewa jihar Katsina tashiga cikin jihohi goma sha uku 13 da zasu samu tallafin kayayyakin a Nijeriya,ya kaara da cewa a halin yanzu Gidan sauron har ya iso cikin jihar.

@katgovmedia ta ruwaito cewa gwamnan ya yabama wakilan da kungiyoyin bisa wannan tallafin kuma yayi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da kyauta aka bada domin ana samun bata gari suna saidawa kamar yadda yafaru a 2014.

Masari ya tabbatar masu cewa zasu samu dukkan goyon baya da hadin kan da suke bukata kuma zaije wajen kaddamar da rabon kayan dakanshi.

Binciken mu ya nuna cewa za’a fara Rabon kayayyakin a satin farkon watan Satunba kuma za’a dauki kwana 4 ana rabon kayayyakin Wanda akalla za’a dauki ma’aikata na wucin gadi 28,000 a fadin jihar ,yin hakan zai taka rawa ga tattalin arzikin jihar.

Director General
katsina Media & Publicity
Ibrahim M Abdullah
27th August 2018

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here