APC ce gidan dake tara Barayin kasa. Inji Sule Lamido

0

APC ce gidan dake tara Barayin kasa. Inji Sule Lamido

Daga Zubairu Muhammad

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma Xan takarar Shugabancin Qasa a shekarar 2019 Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka gaban dubban Jama’a a garin Lafia jihar Nasarawa.

Lamido yace Jami’iyyar APC mai Mulki tazam matattarar tara varayin qasa. Yace; Jami’iyyar APC tace duk wadanda sukayi Mulki a baya Varayine kuma zata ka masu amma da zarar mutum ya sace dukiyan alumman Jihar shi ,sai ya sauya sheka daga wata Jami’iyya zuwa APC sai ya zama mutumin kirki.

Lamido bayyana haka ne lokacin da yaje yakin niman zave, a garin Lafia Jihar Nasarawa. Yace; Gwamnatin dake Mulki ta maida EFCC kare farauta tana mata farautar Varayi.
Yace; da EFCC akeyiwa mutum barazana a bayyana masa abinda yasata akuma cedashi ko yadawo APC ko a kamashi..
Yace; anyi haka da Ujo Kalu sannan anyiwa Tsohon Gwamnan Akwai-Ibom . Lamido yace; anyiwa tsohon Gwamnan varazan Xan haka yabi Buhari zuwa London Buhari ya tabbatar masa cewa idan ya dawo APC babu abinda zai faru dashi.

Ya kara da cewa; akwai ire-iren Su dayawa wadanda sukayi mulki kuma suka sace dukiyar Jihar wasuma babu aikin kirki dasukayi a jiharsu amma yanzu su mutanin kirkine saboda suna APC.

Sule Lamido yace; a shekarar 2015 idan wani yace; sai Buhari idan kace dashi ayi adu’a Allah ya zave mana mafi alheri sai ace dakai Arne, xan kudu. Amma yanzu da Buhari yake mulki alumma sunaji a jikinsu, da dama suna danasani.

Saboda babu ayyukan alheri da Gwamnatin Buhari ta kawo sai dai kara barnata dukiyar qasa. Yace; Buhari yayi alkawura dayawa kafin a zaveshi cikin su harda abubuwa uku da ace zai samar dashi.
Tsaro – Tattalin arziki – Yaki da cin hanci da rashawa. Amma yanzu wannene ya samu?

Qasar babu tsaro ko kadan harma gara Gwamnatin baya. Yanzu kashe – kashe ya yawaita idan kaje Maduguri kullun kisan alumma akeyi ga Zamfara ga Benuwe ga Nasarawa ga Taraba ga Adamawa ga Niger. Ya kara da cewa ; yanzu saboda lalacewa da rashin sanin hakin yan qasa. Mutum bai isa yabi wasu hanyoyi a qasan nan ba sai ya gamu da masu sace mutani. Yace ; hata hanyar Abuja zuwa Kaduna babban abin kunya sace mutani akeyi babu dare babu rana.

Ya kara da batun yadda tattalin arziki qasa ta lalace alumman qasa suka shiga cikin wahala talauci yanwa tsadar rayuwa.

Gwamnatin Buhari cinhanci da rashawa ya mamayeta babu abinda Ministochi keyi sai facaka haka Gwamnonin APC.

Da yake zantawa da Wakilin Leadershipayau bayan kammala taron. Da aka tambayeshi makasudin tsayawarshi takara. Yace; saboda ” in xan Nijeriya ne ina da daman tsayawa takara kamar yadda tsarin mulki ya bani dama haka yaba kowa dama.
Duk xan qasa yana yancin yin takara saboda yabada gudumawarsa .

Da yake amsa tambayar kozai iya kawatanta wanan Gwamnatin ta APC data PDP sai yace; a tambayi Jama’a saboda yanzu kowa na gani yana kumaji a jikinsa ko a rigar sawa kawai da abinchi da kwanciyar hankali yanzu alumman qasane zasuba da labari yaya bambamcin yake.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here