Mahara suna kashe  masu bada kayan agaji na Duniya

0

Mahara suna kashe  masu bada kayan agaji na Duniya

Daga Zubairu Muhammad

A ranar 19ga watan Agosta ne Majalisar Dinkin Duniya take bikin tunawa da Ma’aikatan ta na agaji guda  22 da aka kashe sama da shekaru goma sha biyar a Babban Birnin Bagadad ta qasar Iraki .
Yadda aka sanyawa ranar suna da cewa ranar masu niman agaji ta masamman a duniya.
Da yake jawabi kan wanan ranar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr.Antonio Guterres yace; ”
A wannan shekarar ta tunawa da masu neman agaji, wanda aka fara fiye da shekara Sha biyar, tunlokacin da aka kaima wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu ba da agaji a garin Baghadad ta kasar Iraq, a ina aka kashe mana abokan aikinmu su 22 . To, tun daga wannan lokacin muka mai da wannan rana ta zama ranar masu ba da Agajin gaggawa ta Duniya.”
Yanzu haka muna da kididdigan Sama da Mutane 4,000 a Duniya masu aikin ceto, wadanda aka kashe su. Muna kuma da adadi masu yawa wadanda aka jikkata, ko aka yi garkuwa dasu.
Dan haka yanzu a duk shekara mu kansami adadin masu ba da agajin gaggawa sama da 300 wadanda ake kashewa, ko a jikkata su ko kuma ayi garkuwa dasu.

Farar hula su ake kashewa a duk wani rikici da ke faruwa a Duniya. Yanzu kashe kashen ma karuwa ya ke yi a Duniya, dan ko shekarar da tagaba sai da muka sami adadin Mutanen da suka rasa rayukan su sama da 26,000, a Kasashe Shida kawai, Afghanistan, Central African Republic, Cango, Iraq, Somalia da kuma Yemen.
Ya kara da cewa ; A fadin Duniya rikici na cigaba da ta’azzara, a inda Mutane ke kara rasa matsuguni, yanzu haka muna da addadin ‘yan gudun Hijira a fadin Duniya wadanda suka kai Miliyon 65, kuma kunlun kara daukar yara ‘yan ta’adda ke yi suna basu horo don cigaba da ta’addanci a Duniya.
Masu bada agajin gaggawa aikin su ne in rikici ya faru su taimaka ma wadanda rikicin ya rutsa dasu, amma abin haushi suma kawai sai kaga ‘yan ta’addan na hadawa dasu.
Dan haka muna kira ga Duniya baki daya da su bamu hadin kai dan ganin an shawo kan wannan mummunar matsala wacce take jawo asarar rayuka sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here