MARTANIN BUHARI GA SHUGABAN AMURKA, DONALD TRUMP.

0

MARTANIN BUHARI GA SHUGABAN AMURKA, DONALD TRUMP.

Furucin shugaban kasar Amurka mai kama da izgili ga shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya yamutsa hazo irin na siyasa. A cikin furucin nasa wanda aka saki a shekaranjiya litinin, Trump ya bayyana cewa; Buhari da shi da gawa sammakal. Kuma ba ya kaunar ya sake haɗuwa da Buhari ko sau ɗaya a rayuwarsa. Domin yana yin mu’amala ne kawai da shugabannin da suka cancanci a yi mu’amala da su.

Buhari ya mai da martani da cewa, “shugaban kasar Amurka ya yi furucin ne cikin fushi. Saboda na ce ba zan ba wa kasarsa man fetur ba”. Ya kara da cewa, “ziyarar da nake yi zuwa kssar Amurka ina yin ta ne don ganawa da Trump a samar da hanyoyin da za a haɓaka harkar tsaro a kasashen Najeriya da Amurka. Amma sai shi Trump ɗin ya ɓige da rokon na taimaka na ba wa kasarsa mai, ni kuma na ki amincewa”.

Daga karshe, Buhari ya kalubalanci Trump da ya faɗa masa yadda aka yi shi Buharin ya yi tafiya har ta tsawon kilomita 800 zuwa filin idi, idan har da gaske shi gawar ne kar yadda Trump ɗin ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here