Siyasar Adawa: Me Ya Sa Magoya Bayan Saraki Ke Kyarar Sanata Abdullahi Adamu?

0

Alamu sun bayyana cewa tukunyar siyasar 2019 za ta fi sauran tukwanen siyasar kasar nan tafarfasa. Hakan ta sa aka yi ittafakin cewa tun daga dawowar mulkin dimokuradiyya Nijeriya a shekarar 1999, ba a taba samun wani yanayi da ya zafafa harkar siyasa kamar wannan lokacin ba.

Masu fashin baka na harkar siyasar kasar nan sun tabbatar da cewa matukar ba a yi wa tufakar hanci ba, shakka babu za a fara dauki-ba-dadi a tsakanin manyan ‘yan siyasar kasar, musamman ma da a yanzu an shata layi tsakanin jam’iyya mai mulki ta APC, a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wadda a yanzu ta soma farfadowa, tare da karbar wasu bakin membobi daga APC.

A daidai lokacin da ake tsaka da wannan bahallatsar ta siyasa, kwatsam, wasu daga cikin sanatocin da ke goyon bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, wato Sanata Abdullahi Danbaba (dan jam’iyyar PDP daga Sokoto) da kuma Sanata Isa Misau (na jam’iyyar PDP daga Bauchi), suka bayyana abokin aikinsu, Sanata Abdullahi Adamu (dan jam’iyyar APC daga Jihar Nasarawa) a matsayin jagoran masu haddasa rarrabuwar kai a babbar majalisar ta dattawa.

Koda yake dai, wannan wutar rikicin ta fara ruruwa ne tun gabanin lokacin da Sanata Abdullahi Adamu ya fito firi-falo ya bayyana jinjina game da goyon baya ga Shugaba Buhari, inda ya nuna cewa, duk lalacewar goma dai, ta dara takwas! Sanatan ya kan bayyana manyan muradu da ci gaban da APC ta samar da Nijeriya a cikin shekaru uku kacal, inda yake yin tir ga masu saurin canza sheka zuwa PDP, a matsayin masu son rai ne da neman abin duniya.

Bincike dai ya nuna cewa irin wadannan kalaman da Sanata Abdullahi Adamu ne suke fusata dukkanin wadanda suke goyon bayan jam’iyyar ta adawa, wato PDP. A gefe guda kuma, a baya-bayan nan da shugaban majalisar ta Dattawa, Bukola Saraki ya fice daga APC zuwa PDP, husumar ta kara yin zafi, inda majalisar ta dare gida biyu.

A yayin da sanatocin ke ci gaba da bayyana Sanata Abdullahi Adamu a matsayin mutumin da ya zamo mai bin yarima ne don ya sha lagwada a hannun jam’iyya mai mulki, tuni kuwa rahotanni sun bayyana dimbin goyon bayan da Sanatan na Jihar Nasarawa ke ci gaba da samu daga al’ummar Nijeriya, musamman ma talakawa.

Irin goyon bayan da ake yi masa kuwa, ba ya rasa nasaba da yadda ya jajirce wajen marawa Shugaba Buhari baya, gami da yin kira ga dukkanin’yan kasa masu kishin kansu da su tabbatar sun cire son rai, sun nemar wa wannan kasa – Nijeriya mafita, daga wadanda ake ganin sun gaji da tsarin da Shugaba Buhari ya kawo a Nijeriya na hanyoyin tsaftace kasar daga halin da take ciki.

A wani rohoton kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya kara mika jinjina ga Sanata Abdullahi Adamu a daidai lokacin da ya gudanar da bikin cikarsa shekaru 72 a duniya. Shugaba Buhari ya bayyana sanatan a matsayin daya daga cikin dattawan da wannan kasa tamu za ta ci gaba da alfahari da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here