‘YAN SANDA SUN AZABTAR WANI TELA HAR LAHIRA.

0

 

‘YAN SANDA SUN AZABTAR WANI TELA HAR LAHIRA.

Dangin wani tela mai suna Bashir Muhammad suna neman hakkinsu a kan mutuwar da ya yi sanadiyyar dukan kawo wuka da jami’an ‘yansanda suka yi masa.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an sun iza keyar Bashir ne, a yayin da yake cin abinci tare da ɗan’uwansa a gidansu. Suka ce suna tuhumarsa da sayen kayan sata wanda ya riga ma ya ba da adbas ɗin kuɗi Naira 1,500 daga kuɗin kayan. Inda suka tafi da shi caji ofishinsu dake yankin Kofare dake Yolan jihar Adamawa.

Wani wakili daga dangin mamacin mai suna Ribadu Mustafa ya bayyana cewa, Bayan jami’an sun sa masa ankwa, sai suka garkame shi. Wani ɗansanda mai suna Kaka ƴshi ya yi ta dukan Bashir har sai da ya daina motsi. Ya kara da cewa, washegari da ɗan’uwansa ya je kai masa abinci, shi ma sai suka garkame shi a wani dakin daban. Danuwan nasa ya bayyana cewa, ya yi jiyo ihun Bashir a lokacin da ‘yan sandan ke ta azabtar da shi.

Da suka ga ya jikkata da yawa, sai suka yi maza suka mika shi asibiti inda asibitoci biyu suka ki karɓarsa sai na uku ne ya karɓe shi saboda ganin yadda al’amarin ya ɓaci. A asibiti na uku ne aka kwantar da shi yana amsar magani har dai ya kai takarda wato ya ce ga garinku.

Ribadu ya kara dacewa, ‘yan sandan sun azabtar da shi ne, ba tare da sun zurfafa bincike a kan al’amarin satar. Don haka yake kira da babbar murya ga hukumar tsaro ta jihar da su yi adalci su hukunta waɗannan ɓata-garin ‘yansandan. Domin a cewarsa aikinsu shi ne, bincike a kan laifi ba su da hurumin dukan mai laifi. Ya kara da cewa, sam jami’an basu yi bincike ba kafin su fara jibgar Bashir.

Har yanzu dai
Kwamishinan ‘yansandan jihar Adamawa, Abdullahi Ibrahim bai ce komai ba a kan al’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here