KUDI SUN RABA KAN YAN FIM A KATSINA

0

KUDI SUN RABA KAN YAN FIM A KATSINA

Daga ISAH BAWA DORO
a Katsina.

A cikin watan da ya gabata ne aka riƙa ganin ‘yan fim ɗin jihar Katsina suna ran gadi a gidan gwamnatin jihar, lamarin da jawo ce-ce-ku-ce har yasa wasu suka fara karatun zuci suna tambayar zuciyar su wai mai ya kai su?

Jarumi kuma mawaƙi, Yusuf Haruna wanda aka fi sani da “Baban Chinedu” shi ne mutum na farko da ya fara yi wa jaruman Finafinan Hausa na jihar Katsina jagoranci zuwa gidan gwamnati. A ranar 6 ga watan Yuli ne dai wasu daga cikin ‘yan fim ɗin jihar Katsina aƙalla 36 daga shiyoyyin Daura da Funtuwa da kuma Katsina suka halarci gidan gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagoracin Baban Chinedu.

Da ya ke yi wa Mujallar fim bayani game da yadda ya jagoracin ‘yan fim ɗin har suka gana da mai girma gwamnan Katsina da kuma abin da suka tattauna, Baban Chinedu ya ce: Ya sha ya haɗu da wasu daga cikin ‘yan fim ɗin jihar Katsina suna riƙe da takardun su suna so su ga gwamna, sun sha zuwa su kai takardar neman amincewa a gana da su amma suna tunanin kamar takardun ba su isa a wurin sa, ni kuma na yi masu alƙawarin duk ranar da Allah ya sa muka haɗu da shi zan yi masa bayani. Ranar da Allah ya sa muka haɗu da shi na yi masa bayani na ce akwai wasu ‘yan fim na Katsina da suke so su ganka, sai ya ce to in-sha Allah zan gan su. A lokacin da ya sanya mana rana, shi ne na kira Aminu Mannir Ke-eza da Binta Kofar Soro na ce masu su haɗa mana ‘yan fim ɗin jihar Katsina waɗanda suke zaune a cikin gari, ba waɗanda su ka yi suna a waje irin mu ba, wanda da su ne mu ka yi tafiyar.

Baban Chinedu ya ci gaba da cewa: Kuma mun je mun ziyarci gwamna ya karɓe mu hannu biyu. Sannan ya ce a shirye ya ke da ya taimaki dukkan wani mai sana’a domin ƙara masa ƙarfi. Bayan sun gama ganawa daga ƙarshe ya ce washegari su zo su karɓi kuɗin mai wanda ya basu naira miliyan ɗaya. Daga cikin waɗanda suka je taron sun haɗa da: Yusuf Haruna Baban Chinedu, Abdu Boda, Aminu Dagash, Aminu Mannir Ke-eza, Ibrahim Wisdom, MJ Saulawa, Binta Kofar Soro, Binta Ola, Abu Waziri, Rabi’u M. Yaro, Hajiya Bilki, Lawal Sa’idu Washasha da sauran su.

Sati ɗaya kacal da ziyarar ta su, sai kuma a ranar 12 ga watan Yuli aka ƙara ganin wata tawagar ‘yan fim ɗin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Binta Kofar Soro, sun ƙara kaiwa gwamna wata sabuwar ziyarar, ya yin da wasu ke tunanin tsegumi tare da guna-guni da aka samu ta waccan tafiyar ta farko shi ne ya haifar da wasu ‘yan fim suka umarci Binta Kofar Soro da ta sake yi masu wani jagorancin zuwa gidan gwamnati. A wani Bincike da Mujallar Fim ta yi ta gano cewa sabuwar ziyarar da aka sake yi ƙarƙashin jagorancin Binta Ƙofar Soro, ziyara ce ta musamman wadda ta haɗa Furodusoshi masu zaman kan su waɗanda suke shirya Finafinai a ƙarƙashin kamfanin nin kan su. Da ta ke yi wa Mujallar Fim ƙarin bayani game da ziyarar shugabar tafiyar, Hajiya Binta Kofar Soro ta ce: Ziyarar da mu ka yi ziyara ce ta mu Furodusoshi masu zan kan su, muna da rijistar kamfani, muna zuba jarin mu mu yi fim da kuɗin mu, sannan mu ne muke haɓɓaka harkar fim a jihar Katsina har kowa ya san da ita. Hakan yasa mu ka yi gayyaci shugaban jarumai Alhassan Kwalli saboda shi ya san aikin da mu ke yi kuma muna kiran sa aiki, ya yi mana wannan rakiya zuwa wurin gwamna. A ziyarar ta su, su ma Gwamnan Katsina ya karɓe su hannu bi-biyu kuma ya ce a shirye yake da ya taimake su.

Sai dai Wata majiya ta tabbatar mana da cewa Gwanan ya umarce su da su yi kungiya ɗaya, wadda za ta zamo ta tattara duk wani mai ruwa da tsaki a jihar a harkar fim na Katsina. Wanda su ma gwamnan ya ba su naira Miliyan ɗaya. Da alamu dai ziyarar ta su za ta bar bayar da ƙura ganin yadda gwamnan ya umarce su da su haɗe wuri ɗaya. Wasu na ganin ziyarar ta biyu kamar kishiya ce aka yi wa ta farkon hakan yasa ake ganin cewa zai yi wuya su haɗe wuri ɗaya saboda ko bayan dawowar su ba a ƙara jin kwamitin da suka yi ziyarorin sun shawarcin juna wurin yin maja ba.

Da ya ke yi wa Mujallar fim ƙarin haske game da tafiyar, mai magana da yawun ƙungiyar da suka yi ziyara ta biyu, El Zaharadden Umar ya wanke kan su daga zargin da ake yi masu na cewar sun yi wa tafiyar farko kishiya, inda yace waccan tafiyar daban, ta su daban, manufofin waɗancan daban, su manufofin su daban, ya kuma ce babu inda gwamna ya ce su haɗu da waɗancan a matsayin inuwa ɗaya.

Ya ƙara da cewa, kamfanoni masu zaman kansu ne suka kaiwa mai girma gwamna ziyara na nuna goyon baya bisa shirye-shiryen gwamnatin sa, da kuma yadda za ai ita wannan gwamnati ta taimakawa waɗannan kamfanoni domin su ci gaba da huɗɗoɗin su kamar yadda suka saba.

A cewar sa, sanin kowane an samu taɓarɓarewar tattalin arziƙi wanda yasa kamfanoni basu iya ba su iya finafinai kamar yadda suke yi a da, ganin wannan gwamnati tana taimakon irin waɗannan kamfanoni tare da lalubo hanyar da za a taimaka su masu a gwamnatance. An yi tafiyar ne ƙarƙashin jagorancin Hajiya Binta Ƙofar Soro. Kamfanonin da su ka yi ziyarar sun haɗa da kamfanin “Ƙofar Soro Film Production” wanda yake a ƙarƙashin Binta Ƙofar Soro, sai kuma kamfanin “Bluesound Studio” na Balarabe Kabir, sai kamfanin “Bizee Network and Production” na Bashir Ahmad Bizee, sai kamfanin “M. Yaro Sound Studio & Entertainment” na mawaƙi Rabi’u M. Yaro, sai kamfanin “Ɗan Ghali Multimedia” na Ghali T. Yusuf, sai kuma kamfanin “Koli Trading Company” na Isma’il Koli, da kuma kamfanin “Dankama Media Concept Limited” na El Zaharadden Umar.

Yanzu haka dai waɗanda suka yi tafiyar farko sun sanyawa ƙungiyar su suna “Masari Film Makers” wadda har sun fara yi wa gwamna wasu shirye-shirye wanda Aminu Mannir Ke-eza ya bada Umarni.

An ciro daga mujjallar fim

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here