AN ZARTAR DA HUKUNCI AKAN MATA ‘YAN MADIGO A KASAR MALAYSIA

0

AN ZARTAR DA HUKUNCI AKAN MATA ‘YAN MADIGO A KASAR MALAYSIA

A yau Litinin wata kotun shari’ar musulunci a Kasar Malaysia ta zartan da hukunci na bulala shida-shida akan wasu mata guda biyu ‘yan Kasar wadanda aka kamasu da laifin aikata Madigo, sannan aka yanke musu taran kudi Ringgit 3,300 kimanin Naira 270,0000 a kudin Nigeria

Tun a watan hudu na wannan shekara jami’an tsaro na Kasar Malaysia wadanda suke aikin jaddada shari’ar musulunci (Islamic Enforcement Officers) suka kama ‘yan matan ‘yan shekaru 22 da 32, an kamasu a cikin mota a wani gurin shakatawa na jama’a suna madigo

Bayan an gurfanar dasu a gaban kotu sun amince da laifin da suka aikata shine alkali ya yanke musu hukuncin bulala shida ga kowacce da kuma tara, sannan alkali yace ayi musu bulalan a gaban taron jama’a dake farfajiyan Shari’ah High Court Kuala Terengganu, domin ya zama ishara ga masu aikata irin wannan kazamin laifi

Sai dai manyan kungiyoyin ‘yan Luwadi da Madigo na duniya sun fito sun bayyana wannan hukunci da aka zartar akan ‘yan matan a wani mataki na rashin adalci da cin zarafi da zalunci, wata jami’a a kungiyar neman ‘yancin masu auren jinsi “Transgender Right Group” mai suna Thilaga Sulathireh tace wannan hukunci da aka zartar akan mata ‘yan madigo zalunci ne, kuma babu abinda zai kara sai fitina da tashin hankali da tunzura al’umma a Kasar

See also  FG reiterates commitment to ensure efficient power supply

Sai dai Ministan harkokin musulunci na Kasar Malaysia yace ba zasu taba kyale duk wanda ya keta hukuncin Allah a Kasar Malysia ba, kasancewar Kasar tana gudana ne akan tsarin dokokin shari’ah na musulunci da kuma na Kasa saboda wadanda ba musulmi ba idan sun aikata laifi a musu hukunci da na Kasa

Abin bakin ciki shine wai har wasu kungiyoyi ake dasu wadanda suke nemawa ‘yan madigo da ‘yan Luwadi ‘yanci a doron Kasa kuma wai a Kasashen musulmi, har a zartar da hukuncin Allah amma su fito suna bayyana hakan a matsayin zalunci, Allah Ya sauwake

Allah Ka shiryar da masu aikata laifin Madigo da Luwadi
Allah Mun tuba kar Ka kamamu da laifin da masu auren jinsi suke aikatawa Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here