INA NAN A PDP BA GUDU, BA JA DA BAYA – SHEKARAU.

0

INA NAN A PDP BA GUDU, BA JA DA BAYA – SHEKARAU.

jiya ne tsohon Gwamnan Jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau Ya tabbatar da matsayarsa game da jita-jitar cewa, zai fita daga PDP ya kafa wata jam’iyyar sabuwa. Ya ba da sanarwar cewa, ko kusa ko kaɗan, ba shi da niyyar barin jam’iyyar PDP. Don haka ya ce ba hannunsa a duk wasu shirye-shiryen samar da wata sabuwar jam’iyya wacce za ta yaki Jam’iyyun APC da kuma PDP.

Shekarau ya yi wannan jawabi ne, yayin da yake mai da martani a ka jita-jitar da take ta yaɗuwa na cewa, wasu jiga-jigai daga PDP ɗin za su ɓalle daga tafiyar, domin kirkirar wata sabuwar jam’iyyar. Shekarau ya karyata wannan batu. A yayin hirar sa da ‘yan jarida ta bakin mataimakinsa a kan harkar yaɗa laɓarai, Gali Saddiq.

Inda ya kara da cewa; “ina son al’ummar jahar nan su sani har yanzu ni ɗan jam’iyyar PDP ne. Kuma ba ni da niyyar barin jam’iyyar ballantana a yi zancen kirkirar wata sabuwar jam’iyyar”. Tsohon ministan ya ci gaba da cewa; “Ban taɓa gaya wa wani ba ko kuma mu yi taron ganawa da wasu don shirya yadda za a kirkiri sabuwar jam’iyya. Sai dai a kwanakin nan ni da wasu masu kishin jam’iyyar mun yi tarurruka da dama don warware matsaloli da samar wa jam’iyyar mafita a kan dalilin da ya sa ta sha kaye a hannun APC a kakar zaɓe ta 2015.”

See also  Tinubu Ya Ce Ba Zai Janyowa Najeriya Yaki Ba

Ya kara da cewa makasudin ganawarsa da Masu kishin jam’iyyar shi ne a samu maslaha da daidaito tsakanin ‘yan jam’iyyar. Wannan da kuma cigabanta su ne babban abinda jam’iyya ta sa gaba a halin yanzu.”

Shekarau ya ci gaba da cewa; “Watanni biyar da suka wuce, Shugabancin PDP ya naɗa wani kwamiti mai kunshe da mutane 15 domin a samo mafita ta din-din-din a game da matsalolin da suke addabar jam’iyyar. A matsayin mamban kwamitin mun saurari korafai fiye da 500 kuma har ma mun rubuta rahotonmu mun aike wa uwar jam’iyyar PDP.
“A maysayina na mamban kwamitin gyaran jam’iyyar, don me zan bar jam’iyyar ba tare na na ji hukuncin da ta yanke ba? Don haka matsaya ta ita ce har yanzu ina nan a jam’iyyar PDP kuma ba ni da niyyar fita daga cikinta, ko kuma shirin na kirkiri wata sabuwar jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here