Dailin Da Ya Sa Shekarau Ya Fita Daga PDP, Ya Koma APC.

0

Dailin Da Ya Sa Shekarau Ya Fita Daga PDP, Ya Koma APC.

Bayan ya daɗe yana musanta zancen komawarsa APC, Sai ga shi a yau Talata Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim ya bayyana fitarsa daga PDP da kuma komawarsa APC.
Shekarau ya bayyana hakan ga ‘yan jarida ta bakin jami’insa na hulɗa da ‘yan jaridu, Alhaji Sule Ya’u Sule.

Shekarau ya fita daga APC a shekara ta 2014 saboda rashin adalcin da ya ce ana yi masa a cikin jam’iyyar. A inda ya koma PDP.
Yanzu kuma sai ga shi ya sake komawa APC.

Dalilin komawarsa APC ba ya rasa nasaba da rikicin cikin gida da ya kunno a cikin PDP. Na yadda uwar jam’iyyar ta jiha ta zama ‘yar amshin shatan Kwankwaso Inda a kwanan nan uwar jam’iyyar ta kasa ta rushe shugabancin jam’iyyar na jahar kano. Wannan ya ba wa kwankwaso damar rarraba mukaman jam’iyyar ga mabiya ɗarikar kwankwasiyya.
Wannan ya sa da shi Shekaran, da Aminu Wali da Bello Hayatu Gwarzo suka ɗunguma zuwa kotu amma uwar jam’iyyar ba ta fasa abinda ta yi niyya ba. Domin ta zamo ‘yar amshin shatan Kwankwaso.

Rahotanni sun nuna a jiya ma Shekarau da su Bello Hayatu Gwarzo sai da suka sake yin tattaki izuwa sakateriyar jam’iyyar dake Abuja. Da alama dai irin tarbar da suka samu a can shi ne ya yi sanadiyyar fitar Shekarau daga PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here