Da mun sayi kuri’a da mai maganar baici kauyensu ba…da har shi sai mun saya…inji Gwamnan katsina Aminu Bello Masari

0

RAHOTO NA MUSAMMAN
Da mun sayi kuri’a da mai maganar baici kauyensu ba…da har shi sai mun saya…inji Gwamnan katsina Aminu Bello Masari
Daga wakilan taskar labarai.
Gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari.ya mai da martani ga zargin da shugaban PDP na jahar katsina yayi da yace a zaben cike gurbin yankin daura APC ta sayi kuri u.! gwamnan da yana magana. A wajen taron masu ruwa da tsaki na jam iyyar na jahar, yace wani yace wai mun sayi kuri u..shi mai maganar ai yaci kauyensu..wanda inda sayen kuri u muke da bai ci kauyensu ba.ba wai kuri un kauyen nasu ba..da har shi muna da kudin da zamu sayen shi.
Amma bamu yi ba a maimakon haka jama a ne suka fito tsakaninsu da Allah suka nuna wa APC kauna.kuma suka jefa mata kuri a
Gwamnan yayi godiya ga yan jam iyyar APc da suka fito suka farantawa shugaban kasa rai.wanda suka zabi dan takarar jam iyyar
Da yake magana akan matsayar da jahar katsina ta dauka.na yin zaben fitar da yan takara.a tsarin wakilai ba na ..kato bayan kato ba.wanda kowa na iya bin layi
Yace ko a abuja .matsayar da aka tsaya shine.kowace jaha ta fitarwa da kanta tsari.duk kuwa da cewa.shugaban jam iyyar Adam ashimolu yazo da ra ayinshi na yi fitar da dan takara a tsarin kato bayan kato
Wanda sai da ya dau mintuna yana bada muhimmacin a yi zabe kato bayan kato .amma bai bada bayanin illarsa ba.
Gwamnan yace mu munje jaharsa .lokacin da za ayi fitar da dan takarar gwamna adams yana gwamna amma tsarin da akabi a jahar ta edo tsarin wakilai su fitar da dan takara ne.kuma shi akabi
Gwamnan yace a taron majalisar zartaswa na APC an tsaya akan kowace jaha taje ta fitar da tsari dai dai da ita.kuma kamar yadda tsarin mulkin jam iyyar ya shata
Gwamnan ya cigaba da cewa.bayan an baro abuja sai wani jami i a ofishin jam iyyar ya fitar da wata sanarwa.wadda baccin Allah ya kiyaye dattawa a jam iyya sun maza sun shiga maganar.da ta zama wata babbar fitina a jam.iyyar ta APC amma sai aka dau mataki kuma yayi amfani.
Gwamnan yace duk jihohi sun fitar da matsaya ..saura mu.kuma yau komai dare.dole uwar jam iyya su san matsayin mu.
Yace mun kira taron da ayi bayanin matsayoyin guda biyu.kuma a tattauna .yace jahar katsina nan ne gidan shugaban kasa.kuma yana sane da abinda ke faruwa fiye da kai da kake cikin jahar zaune
Gwamnan ya kara da cewa.duk tsarin suna da amfanin su da nakasu. Yace zaben fitar da dan takara ta wakilai akwai cin hanci.deligate na amsar kudi.haka shugabannin jam iyya
( anan take sai gwamnan ya kalli malam shitu dake gefensa a zaune)
Gwamnan yace .shi kuma na kato bayan kato.yana da tsada.wajen aiwatarwa.ga babu tabbaci su wa ke layi naka ne ko nasu?
Gwamnan ya kara da cewa duk matsayar da aka yarda kowa zai sa hannu da sunansa sa lambar waya.wanda za a hada da takardar a kaima uwar jam iyya.
Yace. Yin haka ya zama wajibi.don hujja don ba wanda ya san zuciyar wani sai Allah!
Gwamnan ya kara da cewa.yanzu ga Abdulmanaf nan ji nake kamar in hadiye shi don kauna.amma kila shi a zuciyarsa in bashi bindiga aka ce ya harbe wani ni zai harba.
Duk dakin taron ya barke da dariya
Daga nan taron ya dau matsayin cewa.katsina zata fitar da dan takarar ta .ta hanyar wakilai ne..kuma aka sa hannu a haka
Taron kuma ya jaddada cewa gwamna Aminu bello masari da shugaba Buhari sune yan takararsu a jam iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here