KO SANATA ABU IBRAHIM ZAI IYA TAKARA?

0

KO SANATA ABU IBRAHIM ZAI IYA TAKARA?

Daga wakilan Taskar labarai
Wani bincike da jaridar Taskar labarai tayi shine yiyuwar tsayawar takarar Sanata Abu ibrahim Sanata Mai wakiltar shiyyar Funtua a jahar Katsina.. binciken mu ya gano cewa sanatan Mai shekaru saba in da uku a duniya..Wanda kuma yasha gwagwarmaya kala kala na cikin matsanancin Rashin lafiya..Wanda har ta Kai wani sashe na jikinsa baya aiki.
Binciken da mukayi ya tabbatar da cewa .sanatan ya fara kwanciya a wata asibiti a Abuja Wanda kuma aka Sanya kula da tsaron da Babu Mai iya ganinshi sai na kusa dashi.na kusan ma kusa can karshe
Binciken mu ya tabbatar da cewa.. kwanakin baya da wata tawagar gwamnan Katsina taje duba shi a asibitin..hana kowa Shiga akayi..sai gwamnan Katsina kawai Alhaji Aminu Bello Masari..kuma da ya fito bai fadawa kowa halin da ya iske sanatan ba.
Binciken mu. Ya tabbatar yanzu Haka sanatan Yana wani asibiti..dake tsakiyar birnin landan.yana amsar magani da kulawa.
Jaridar Taskar labarai ta aika da wasika ga asibitin ta hanyar email..Don sanin halin da sanatan ke ciki.amsar da jaridar ta samu daga asibitin shine ,”Bamu amsa ko wace Tambaya Akan maras lafiya dake wajenmu.don Haka duk wata Tambaya da kuke da ita akan wani maras lafiya dake wani asibiti a burtaniya..to ku tuntubi iyalansa ko wadanda suka kawo shi.
Jaridar ta gano iyalan wasu. Daga cikin iyalan sanatan sun fi bukatar ya huta da takara ya zauna ya Zama dattijo a cikin siyasa Wanda ake sauraro.masu wannan ra ayin suka a cikin iyalin suka matsa Masa ya jingine ra ayinshi na Zama gwamnan Katsina..kuma ya amince
Amma ya ce.zai gaba da rike kujerar sa ta dattawa Domin ita dama ance ta dattawa ce kuma shi dattijo ne.tun da ya haura shekaru Saba in.
Yanzu da wannan Rashin lafiya ta same shi..duk gidansa na siyasa sun Shiga turaddadin minene makomarsa .na takara da siyasa? Haka iyalinshi.?
Wata majiya tace wannan shine ake ta muhawara tsakanin iyalin da gidansa na siyasa.
Sanata Abu ibrahim shine Dan siyasa mafi karfi da aka tabayi a yankin Funtua..yanzu Haka mutanensa ke rike da duk mukaman jam iyyar APC gam a yankin ta funtua.wani yace tasirinsa a siyasa a baya ..ba a taba samun kamarsa ba..gaba kuma sanin gaibu sai Allah.
Yanzu Haka masu neman mukamin Sanata a yankin sai tururuwa..a lissafi sun Kai ashirin Amma sai kammala sayar da fom za a iya tantancewa…
Masana siyasar yankin in Abu ibrahim yace ba zai takara ba..duk Wanda ya marawa baya shine zai iya samun tikitin tsaya wa a APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here