AN GARKAME WASU MA’AURATA SABODA LAIFIN TILASTA ‘YA’YANSU SU YI AZUMI.
Wasu ma’aurata Kehinde Omosebiy mai shekaru 48 da Titilayo Omosebi mai shekaru 47 sun shiga komar jami’an ‘yansandan Amurka saboda laifin hallaka ɗansu da suka tursasa wa yin azumi har na kwana arba’in.
Waɗannan ma’aurata suna zaune ne a yankin Wisconsin a kasar Amurka. Kehinde ya yi ikirarin yana da alaka da wata coci wacce ta ba shi mukami kuma ta yi masa umarnin su yi azumi 40 da shi da iyalinsa. Shi ne suka fara tare da matarsa da ‘ya’yansa maza masu shekara 11 da 15.
Shugaban hukumar ‘yansandan yankin Reedsburg mai suna Timothy Becker ya bayyana cewa Kehinde ya zo ofishinsu ya kawo musu rahoton mutuwar babban ɗansa. Koda suka rankaya suka je gidan nasa, sai suka tarar da bayan ɗan nasa da ya mutu ita kanta matarsa da kuma karamin ɗan nasa a jigace suke. Saboda tsananin yunwa da kishirwa.
Becker ya ce; Kehinde na zaune a wani gida ne da ba lamba, kuma ba shi da wayar hannu ga shi ba komai a gidan, ko da abinci ne babu. Amma Kehinde ya gaya wa jami’an cewa sun sayar da kayan gidan ne don yana son su koma Kasar Atlanta da zama shi da iyalinsa. Jami’an ‘yan sandan sun karyata ikirarin da ya yi na cewa azumin yana da alaka da wata coci. Kuma ƙlaifin da kehinde da matarsa suka aikata hukuncinsa shekaru 37 ne a gidan sarka.
A halin yanzu dai an mika karamin ɗan nasu zuwa asibiti domin amsar magani. Ita kuma Titilayo ta ki amsar magani saboda wasu dalilai da suka shafi adɗinin nasu. Don haka a ƴhalin yanzu tana can a kulle a gidan kaso.