BA NAKASASSHE SAI KASASSHE

0

BA NAKASASSHE SAI KASASSHE

Waɗannan hotunan wani dattijo ne, wanda rashin ji da gani da shanyewar hannu guda ba su hana shi yin noma kowacce shekara ba.

Dattijjon wanda aka fi sani da Baba, yana da shekaru 71 da haihuwa. Kuma manomi ne mai kokarin gaske. Majiyarmu wadda wata matashiya ‘yar bautar kasa ce, ta yi tattaki zuwa kauyen da yake a yankin karamar hukumar Lau, dake jhar Taraba. Ta tattaunana da wannan dattijo mai ban al’ajabi. Wanda kurma ne, kuma makaho. Sannan kuma hannunsa na hagu a shanye yake. Amma wannan bai hana kowacce shekara Baba ya noma shinkafa da masara domin ya ci da kansa da kuma yaransa goma sha huɗu da ɗanuwansa ya mutu ya bar masa.

Baba ya rasa idanuwansa tun yana ɗan shekara 13. Amma hakan bai sa zuciyarsa ta mutu ba. Kamar yadda muke gani a kasar Hausa. Nakasasshe ba ya komai sai bara.

Da fatan labarin Baba zai zama darasi ga dukkan matasa, waɗanda Allah ya ba wa rai da lafiya, karfi, da ji da gani. Amma maimakon su yi sana’a, sai su ɓige da yin maula da raraka da tumasanci. Ko kuma su dinga jira sai gwamnati ko wani ya ba su aikin yi. Mu farka matasa!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here