JAHAR KATSINA TA KAUCEWA ZAƁEN MUTUM BAYAN MUTUM

0

JAHAR KATSINA TA KAUCEWA ZAƁEN MUTUM BAYAN MUTUM

Daga Bishir Suleiman

Tun bayan kammala taron ƙasa na jam’iyyar APC, wanda ya haifar da ɗarewar sabon shugaban jam’iyyar Adams Oshimole gadon mulki, ya ke ta ƙoƙarin ganin ya ciyar da jam’iyyar gaba da ɗora ta kan turbar da ta dace, wanda zai kyautatawa kowane ɗantakara da gamsar da al’ummar ƙasar kan tabbatuwar canjin da suke ta bagen ganin a wannan gwamnati.

Amma tun da ya bayyana aniyar tasa, a fili ake ta toka sa katsi, kama daga jiga jigan jam’iyyar da manyan jami’an gwamnati, dan ganin zai shige masu ɗaka da ƙudundune.

Ko a makon da ya gabata, uwar jam’iyyar ta ƙasa da masu ruwa da tsaki dake a faɗin ƙasar, sun gudanar da taron tattaunawa, da ya shafe dogon lokaci, dan cimma matsayar hanyar da za a bi dan aiwatar da zaɓen fitar da gwani.

Wanda mafi rinjayen mahalarta taron, sun goyi bayan shugaban jam’iyyar, na aiwatar da zaɓen ta hanyar Mutum bayan Mutum, wanda a kwanakin baya ake kira da ƴar tunƙe.

Hakan, ya ƙara kwarjin jam’iyyar, daga masu zaɓe har ƴantakara, dan kowa na ganin zai iya jaraba sa’ar da za ta kai shi ga samun nasara lashe zaɓe, da kuma baiwa jama’a damar zaɓen wanda suke so kai tsaye, ba ta hanyar wakilai ba.

Amma ƙudurin ya samu cikas daga wasu jahohi, wanda suka haɗa har da jahar Katsina, dan ko a taron masu ruwa tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jahar a ranar alhamis 5/9/2019, Gwamna Aminu Bello Masari ya yi dogon bayani kan mahimmanci da naƙasun salon zaɓukan fitar da gwanin guda biyu, wato, na zaɓen deligate dana mutum bayan mutum ke da shi.

Wanda ya nuna, na daligate shugabanin jam’iyya na taka rawar su yadda suke so, wajen zaɓen wanda jam’iyya ke so.

Yayin da na mutum bayan mutum ke da wuyar sha’ani wajen masu bin layin zaɓen.

Inda daga ƙarshe, ya goyi bayan aiwatar dana delighate a jahar tasa ta Katsina.

Hakan ya sanya da dama daga ƴan takarar cikin su ya ɗori ruwa, murna ta koma cuki, sannan ya rage kara kainar sayen fom daga sabbin masu neman kujerun.

Wanda wasu daga cikin ke hasashen abin da ya faru daga zaɓen jagororin jam’iyyar da ya gudana a ƴan watanin da suka gabata kama daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi dama jahar baki ɗaya.

Fatan dai jama’a a jahar Allah yasa masu zaɓen su zaɓowa al’umma wanda suke su, ba wanda ya cika masu aljihu da kuɗi ba, kamar ya dai yadda Shugaban jam’iyyar na ƙasa ya ke da rajin duk wanda ya zaɓe ka, a zaɓen fitar da gwani na Mutum bayan Mutum, ba ya ki zaɓen ka ba, a zaɓe na gaba daya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here