Wata Amarya Ta Haife A Sa’o’i kaɗan Kafin A Daura Mata Aure.

0

Wata Amarya Ta Haife A Sa’o’i kaɗan Kafin A Daura Mata Aure.

Kamar yadda ‘yan magana kan ce; _’Allah ɗaya gari bab-ban-ban_ ‘. Wani abu da ya faru wanda da a kasar Hausa ne zai iya zama abin Allah wadai saboda ya saɓa al’ada da kuma addinin yankin. Sai ga shi ya zama abin alfahari da barka a yankin Awo Idemili, na jahar Anambara. Inda,wata Amarya mai suna Misis Chinezu Adeolisa ta bayyana wa Duniya farin cikinta na samun sankacecen jariri a ranar ɗaurin aurenta da rabin ranta Mista Odeolisa. Mista Odeolisa ya bayyana wannan al’amari da cewa daɗi kan daɗi ne. Wato alhairai biyu, a lokaci guda. Abin ya farune awoyi kaɗan kafin a fara shagalin ɗaurin auren, sai kawai nakuda ta kama amaryar. Nan da nan aka mika ta asibiti inda ta haife lafiya, ta samu ɗanta namiji. Angon ya bayyana wa majiyarmu cewa, bayan ta haihun ne ya yi maza ya zo ya shaida wa maɗaurin aurensu, kuma a lokaci guda ya roki alfarmar maɗaurin auren nasu ya ɗan kara musu lokaci domin matarsa ta samu ta gyara jikinta ta zo a ɗaura musu aure. Bayan ta fito daga ɗakin haihuwar ne, sai Chineza ta taho gurin ɗaurin auren nasu inda ‘yanuwa da abokan arziki suka taya su murnar wannan shagali har guda biyu. Chinezu ta ce ta cika da farin ciki maras misaltuwa domin da tana ta tunanin yadda za ta yi hidimar bikin ko rawa za tai mata wuya saboda ta yi nauyi, sai ga shi duk abin ya zo mata da sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here