KU TAIMAKA MASA DA ADDU’AH

0

KU TAIMAKA MASA DA ADDU’AH

Daga datti Assalafiy

Sanarwa daga Dr. Idris Ahmed yace kungiyarsu ta Citizens United For Peace and Stability (CUPS) ta samu sako na bacewar wani babban hafshin sojin Nigeria Manjo Janar Idris Alkali

Shi dai manjor Janar Idris Alkali ya bace ne tun bayan awanni 74 da suka gabata, wayoyinshi gaba daya basa tafiya har zuwa yanzu, ya bace ne akan hanyarshi na zuwa Bauchi daga Abuja.
Ana rokon a isar da wannan sanarwan har zuwa masallatai don a saka wannan babban hafshin soji cikin addu’ah akan Allah Ya bayyanashi

Kamar yadda ‘yan uwan shi wannan sojan suka bayar da bayani, sunce Manjo Janar Idris Alkali yana kan hanyarshi na zuwa Bauchi ne daga Abuja a cikin motarshi, to tunda ya iso kudancin Jos sai ya bace sakamakon bin diddigi (tracking) na nambar wayoyinshi da jami’an SSS sukayi bayan an kai musu rahoto

See also  YANZU-YANZU: Ana zanga-zanga kan shirin kawo tsohon shugaban jami'an tsaro na Ganduje a matsayin Kwamishinan Ƴansanda na Kano

Shi dai Manjo Janar Idris Alkali asalinsa mutumin jihar Yobe ne, kuma an taba hasashen zai zama shugaban sojojin Nigeria

Yaa Allah Ka kubutar da wannan bawa naka lafiya a duk halinda ya shiga, Allah Ka tona asirin duk wanda yake da hannu a bacewarsa

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
08/09/2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here