Zamuba da kiwon Lafiya kyauta a Nasarawa

0

Zamuba da kiwon Lafiya kyauta a Nasarawa

Inji Daktan talakawa

Daga Zubairu Muhammad

Tsohon Xan Majalisar wakilai na Tarayya mai wakiltar mazaver Lafia da Obi Hon. Joseph Haruna Kigbu wanda akewa lakabi da (Daktan Talakawa) yace; nanbada dadewaba Asibitin Talakawa zata fara aiki cikin wanan shekarar.

Yace; idan har Allah yasa aka bude wanan Asibitin to Talakawa zasu amfana da kiwon Lafiya kashi 90% cikin 100. Yace; lokacin da nake Majalisar Wakilai ta qasa nayanke shawarar na samar da wanan Asibitin a mazaveta saboda alummana su amfana komai dare dadewa.

Yace; naduba babban damuwar alumma yanzu rashin tallafi a harkan kiwon Lafiya saboda cututuka yana takurawa talakawa kuma zakaga masu cutar basuda kudin magani.
Wannan yasanya na samar da wanan Asibitin saboda da taimakawa alumma ta suma su morewa mulkin Demukurdiyya.

Wannan harkan ta kiwon Lafiya na kwashe shekara da shekaru inayinsa kuma ta sanadiyar hakane alumma sukemin lakabi da (Daktan Talakawa)

Saboda babu abinda zakayi ka taimakawa alumma kamar kabasu Ilumi da kiwon Lafiya saboda shine taimakon mutani .
Ya kara da cewa ; lokacin da nake kan karagar kujerar Xan Majalisar nayi ayyukan kiwon Lafiya a gurare dabam dabam kuma mun gina dakunan shan magani a Karkara saboda jama’a ta .yace; ya zuna a Majalisar Wakilai daga 2011zuwa 2015.
A lokacin da akayi zaven 2015 nace zave amma aka kwacemin na hakura , yanzu kuma na sake tsayawa takara a Jami’iyyata ta PDP. Na saya Fom kuma gashin na kawowa uwar Jami’iyya ta Jihar.

Hon.Haruna Joseph Kigbu ya bayyana haka ne a gaban dubam magoya bayansa a harabar ofishin PDP a garin Lafia.
Yace; na tabbata idan akayi zave Jami’iyyar PDP zatayi gagarumin nasara kuma zamu kara kawo sauyi mai amfani a qasan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here