Abinda ya haddasa tashin gobarar gas a Nasarawa

0

Abinda ya haddasa tashin gobarar gas a Nasarawa

Daga Zubairu Muhammad

A ranar littinine aka samu mummunan Gobarar wutan Gas wanda  yayi sanadiyyar mutuwar mutani sama da goma sha biyar a garin Lafia cikin Jihar Nasarawa.

Gubarar  ya tashine a Natson  Filing Station inda  kamfanin sayar da gas ta Manaco, dake Bukan Sidi garin Lafia suke da zama.
Abinda ya haddasa gubarar shine lokacin da aka sauke Gas daga Motar sai aka tarar tanan tsiyaya ba’akumasan ta ina take tsiyayaba.
Wannan ya sanya Ma’aikatan Kamfanin sukayi saurin sanar da Hukumar kashe gubara wato (kwana kwana) zuwansu keda wuya sukayi bincike amma an kasa hango wajen kuma gashi karuwa yakeyi.
Nan da nan aka umarci mutanin dake gidan Man subar gurin . batare da bata lokaci ba wuta ta fara tashi.

Anan sunyi iyakar kokarinsu na dakatar da wutar a lokaci guda kuma suka rika koran alumma dake tsaye suna kallo.
Amma karfin wutan yayi yawa kuma ruwa ya kare. Nan take suka ranta a guje.

Ba akai minti biyar ba sai wuta ta tashi sai karar fashewar Tukwanan gas kakeji nan danan wuta ya rika watsuwa sama sai kan motochin da ke wucewa da masu tafiya a qasa.
Motochi goma sha uku suka kone  kurmus yayin da Keke Napel biyu suma suka kone sai mashuna guda shida . cikin motochi sha ukun harda motar Tankan  da tazo da gas din da kuma wata karamar tankan gas da Pakas  dauk  suma sun kone kimamnin mutum 40 ne abin ya shafa.

Da yake jawabi Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura ya tabbatar da mutuwar mutum 9 yayin da saura ke Asibiti wasu na Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya dake Abuja sai wadanda ke Asibitin Dalhatu Araf dake garin Lafia.

Gwamnan yace; idan har abin ya gagara Gwamnatin Jihar Nasarawa zata iya kai marasa lafiyar kasar waje domin samar da lafiyansu.
Tun a ranar Littinin da abin ya faru Shugaban Majalisar Dattawa ta kasa Sanata Abubakar Bukola Saraki yazo yakin niman zabe daga nan ya ziyarci Asibitin.

Nan take ya umarci a kwashe marasa tafiyar zuwa Babban Asibitin kasa dake Abuja.
Yayinda sauran ke karban magani a Asibitin Dalhatu Araf dake garin Lafia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here