SHEKARAU YA SAYI FOM DIN TAKARAR MUKAMIN DA KWANKWASO KE NEMA.
A yau ne tsohon ministan ilimi kuma tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sayi fom din takarar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC. Wannan sanarwar ta fito ne saga bakin Salihu Tanko Yakasai mataimaki a harkar yada labarai na Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Inda ya saka hoton Malamin rike da fom din takarar a shafinsa na ‘Twitter’. Ina ya bayyana cewa; “yau Talata Mai girma shekarau ya yanki fom din takarar sanata a APC, Muna sa ran shi be zai karbe kujerar Wanda ya kusa ya zama tsoho, kuma Sanata mai hawa daya kacal, Kwankwaso. jam’iyyar ta ba shi tikitin fitowa kai tsaye Ba tare da hamayya Ba”.
Idan masu karatu basu manta ba, Shekarau ya shigo jam’iyyar APC ranar asabar din nan da ta gabata. Inda gwamnan Kano Ganduje da Shugaban jam’iyyar APC, suka je gidansa don nuna goyon bayansu. Shekarau ya bayyana wa magoya bayansa dalilin da ya bar PDP. Wato saboda yadda shugabancin jam’iyyar suka mai da kwankwaso Dan gaban goshi suke fifita kwankwaso fiye da shi da ma kowa ma a jam’iyyar.