0

DANJUMA KATSINA: JAGORAN FAFUTIKAR ‘YANTA AIKIN JARIDA.

Daga. Muhammad Jikan Sarki Ruma Dan Waire Daga Katsina.

Aikin Jarida, tamkar mutum ne da ke da jiki da ga66ai irin na mutum. Wadannan sassan jiki na bukatar yin aiki yadda ya kamata don rayuwa imgantacciya ta samu.
Yayinda mutum ke bukatar kwakwalwa don yin tunani da zimmar shirya kowane irin al’amari na rayuwa, mai kyau ko akasinsa, aikin jarida na bukatar ilimi da sanin makamar rayuwa don fiddowa Al’umma irin ababen da suke bukatar sani.
Haka kuma yadda mutum ke amfana da ido, kunne, hannu baki da kafa, aikin jarida na amfani dasu wajen samawa Al’umma amsoshi kan wasu abubuwa da ka iya shige masu duhu.
Aikin Jarida na da kayan ciki da ke aiki gaya wajen daidaita duk wani labari ko tsira sharhi don warware zare da abawa kan duk wani rikitaccen lamari.
Bayan Mallakar duk wadannan ababe ne ma’aikacin jarida da gidan jarida ke iya yanke hukunci a kan manufar kafar yada labarun, watau ko fadar gaskiya ko karya, kishin kasa ko 6angaranci, inganta zama lafiya ko wargazashi.
Bisa ka’ida, aikin jarida, musamman labaru na bukatar wani sabon abu, daga gabas ko yamma, kudu ko arewa da mutane ba su sani ba. Ko kuma bayyana wata sabuwar hanya da za a fahimci wani lamarin rayuwa.
Bahaushe ya ce, Kuturu da kudinsa, sai a bar shi ya duma Daginsa cikin kwanon Alkaki, ya zakulo na can kasa mai Zuma sosai, kana ya biya. Don haka ne duk Wanda ya kashe kudinsa ya kafa gidan Radio ko Talabijin ko Jarida, to lallai ne ya samu bakin fada a ji, tare da yayata manufarsa, dadan mai kyau ce ko mummuna.
Shi kuma maaikacin jarida, duk da akwai dokoki da hukumomi masu sa ido kan shiga tsaka mai wuya, saboda duk wanda ya ci ladar Dankuturu, ai dole yai masa aski!
Alhaji Danjuma Katsina, Danjarida ne da aikin jarida ya game masa jiki, ya mamaye masa rayuwa, ya kuma dauke masa tunani da karfin jikinsa. Daga Wakilin Jaridar Almizan, da kuma kafa kamfaninsa na Madaba’a mai suna Matasa Media Link, ko kuma hadahadar Kungiyancin Kungiyar ‘Yanjarida aka fi Saninsa a shekarun baya. Danjuma ya kware wajen hulda da mutane. Sahibi ne ga manyan mutane da Yansiyasa da masu ilimi. A dukkan wadannan fagage ya fita tsara sosai saboda Dabi’arsa ta Ba ya yin Kwai sai da zakara.
Fasahar Yanar Gizo ta ba Danjuma Katsina damar kafa zaure mafi shahara a Jihar Katsina, watau Katsina City News. Dandalin City News na gudanar da huldarsa cikin Harsunan Hausa da Turanci, kuma ya kunshi Manya, Matsakaita da kananan mutane, masu mulki da Talakawa, Maza da Mata, Yansiyasa da Malamai.
Wannan Dandali na da dokoki da hukunce-hukunce. Labarunsa na zuwa daga dukkan 6angarori, kuma ana muhawara tsakanin sassa masu bambancin ra’ayi.
Kokarin Danjuma Katsina na kafa wata sabuwar Jarida ta Yanar Gizo mai suna Taskar Labaru ne ya zaburas da sha’awata ta yin Wannan rubutu.
Taskar Labaru wata dama ce ta samawa mutanen Arewacin Nijeriya masu iya karanta Harshen Hausa su samu Sahihiyar hanyar samu da bayar da labaru, tare da tantancewa tsakanin labarun gaskiya da na karya.
Duk da yake Bahaushe na da rashin Dauriya ta karanta labaru, musamman masu tsawo, auren zumuncin da aka hada tsakaninsa da Wayar Salula da Yanar Gizo ya bada kafa ta samu da karanta labaru, har ma da mayarda martini ta yanar gizo, don haka Taskar Labaru ta Danjuma Katsina ta zo kan kari!
Abin takaici, Mutanen Arewa muna ta koken yan kudu suna mamayemu da neman cinyemu da yaki ta hanyar amshe wasu muhimman madafun iko. Sai dai akasari ba a san tamkar danne Bodari a ka ne ba. Yakin da ake cinyemu da farfaganda, ana gwama kawunanmu da juna, ana rarraba mu, su kuma suna gangamin hada kawunan junansu da tsayarda manufofinsu.
A ra’ayina, muna da Attajirai masu Dimbin Dukiya da Yanjarida gogaggu. Sai dai yanjaridar ba su da jarin kafa gidajen Radio da Talabijin don kare muradun arewa.
Ban ce babu wadannan gidajen jaridu a arewa ba, amma sun yi karanci matuka. Idan muka dubi Gidan Radio da Talabijin na Liberty, da Arewa24, da Vision Radio da Freedom Radio sun isa misalai na yadda ake iya samun nasara.
Bisa Wannan turba ya zamo wajibi a yabawa Danjuma Katsina a kokarinsa na kafa Wannan sabuwar Jarida ta Taskar Labaru.
Idan abu sabo ya zo wa Mata, sukan yi guda har da Shewa. Don haka, Ahayye Aiyururui, Sannu da Zuwa Taskar Labaru!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here