SARKIN MUSULMI YA YI JAWABI GAME DA HATSARIN MOTAR DA DANSA YA YI A CIKIN MAYE.

0

SARKIN MUSULMI YA YI JAWABI GAME DA HATSARIN MOTAR DA DANSA YA YI A CIKIN MAYE.

Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar (lll) a wata sanarwa wacce sakataren masarautar ya Sanya wa hannu ya tabbatar da faruwar hadarin motar da babban dansa Amir Sa’ad Abubakar ya yi.
Rahotanni sun bayyana cewa, Dan sarkin ya yi hadarin mota wanda ya faru kasancewar yana cikin maye. Kuma ya kure gudun motar. Da misalin 12 na rana a kan titin filin jirgin sama Na jihar Sokoto. Sultan din, ya bayyana cewa, yana farin cikin Sanar da jama’a cewa, Dansa Amir yana ci gaba da samun sauki bayan ya yi hatsarin mota da shi da ‘yanuwansa Khalifa Maccido da Zainab Bara’u Isah. Kuma ya gode Wa ‘yanuwa da abokan arzuka da suke ta zuwa yi musu jaje da kuma dubiya. Inda ya fada kamar haka; “muna son mu kara ba da tabbacin cewa, wadanda hadarin ya shafa, suna cikin kulawa kuma alhamdulillahi suna samun sauki”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here