ƘASHIN BAYAN AL’UMMA. ƘARAMAR HUKUMAR KURFI.

0

ƘASHIN BAYAN AL’UMMA.

ƘARAMAR HUKUMAR KURFI.

Assalamu Alaikum, sunana Fadila H Aliyu Kurfi ‘yar asalin ƙaramar hukumar Kurfi gaba da baya, Marubuciya kuma ‘Yar Jalida mai zaman kanta.

Duk da kasancewa ta marubuciya ban taba ɗaukar alƙalamina na yi rubutu kan siyasa ba amma wannan karon jiki na rawa zuciya na azama suka tilasta mani dole na yi tsayuwar aska domin kwato ma Mata ‘yancinsu, na ɗauki haramar shiga lunguna- lunguna da saƙo-saƙo domin taimakon mata’ yan uwana, wanda ba su da da muryar da za ta yi amo domin faɗa ma duniya halin da suke ciki, suna da koke suna da damuwa suna cikin wahala da ƙuncin rayuwa amma babu wanda za su kai ma koken a saurare su, za mu jawo su jiki mu tallata su duniya ta ji halin da suke ciki, za mu zama tsintsiya domin mu share azzaluman ‘yan siyasa masu ci da guminmu wanda muke kasawa mu tsare mu raka a ƙirga lokacin zaɓe don kishinsu da ƙaunarsu kyauta domin aƙida kawai da kuma masu kuɗi da kansu kaɗai suka sa ni sai idan buƙayarmu ta taso a nememu, ba mu da jam’ iyya ko ɗaya sai wanda zai tallafe mu da yaranmu.

Babban dalila na fara tsoma baki a lamarin mata shine; zuwana Ƙaramar hukumata Kurfi, tsananin kishin mata ya ƙara ƙaimi a zuciyata har na ji zan iya yin komai don ganin an tallafi iyayenmu da ‘yan uwansu bayin Allah mata, su ‘yan siyasar sai dai su taka kawunanmu su ci da zufar su sayi gida da motoci a shige birnin tarayya Abuja, sai lokacin zaɓe su kwaso jiki su dawo su watsa ma mutane ‘yar tsaba a kuma zaɓarsu, ‘yar tsabar ma sai wanda suke da alaƙa da su ko da kuma wanda suke da alaƙa da mai rarrabawar, na sa ni tsaf suna mulkin kama karya tuni amma hankali na bai tashi ba sai wannan karon, dasu fa muke haɗuwa gurin zagin wasu azzaluman shugabanni amma kuma da sun hau sai su koma irinsu su manta da kowa da komai, sai hawan jirgirage a lula cikin duniya ayi ƙara’in wanda ba ayi ba zamanin ƙuruciya, haba shuwagabanninmu kuɗin da kuke saka katin waya kaɗai ku kira wanda kuke so da zaku ware shi ku ba mata tallafin sana’a da ya ishesu har ƙarshen rayuwarsu samun abin da za su ciki ma bakin salatinsu, ba fa irin zuƙa-zuƙan motocinku suke buƙata ba a’a ɗan abin ci da sutura ɗan jari kawai, babu wannan sai dai ku yi lamo matsala da yunwa ta matsa ma talaka ya ɗaga ɗan fili ko gidansu na gado ku saya a wulaƙance.

Na je ƙaramar hukumata KURFI ziyara, kalar ruwan da suke sha kuma suke amfani dasu ruwan tafki ne idan rani ya zo rijiyoyi ƙafewa take yi, ga su da kauri kamar damammiyar fura, shekara da shekaru an kasa magance matsalar ruwa, tambayar da na fara yi ma kai na itace, ;wai duk Ciyamomi, ‘Yan majalisu har da na Dattawa wai! da suke mulki tun ina cikin zanen goyo idan sun kasa magance matsalar ruwa kaɗai me suke iya magancewa, me ye amfaninsu, haba Yaya Kantoma, Malam Ɗan Majalisar Jaha, Alhaji Ɗan Majalisar Tarayya da Baba Ɗan Majalisar Dattawa ko kun manta ne? Ruwan tafkin nan da kuka sha kafin mu ingizaku kan kujerunku ku fara shan ruwan roba har yanzu mutanenku na nan na sha, makarantun nan masu karyayyun kujeru wasu ɗaliban ma a ƙasa suke zama, makarantun nan na babu gyara kuma su kuka yi fa, ko kun manta mu ku ka taka izuwa wannan muƙaman, don kun san cewa kun maƙale kuɗaɗenmu ko safka kuka yi akan kujerunku ba za ku dawo mana ba bare a sha ruwan tafkin nan daku, kun ci ganye, kun mance sanda ake zama majilisa ana koken wasu da ku kuma gashi ana yin naku, mu fa ba gashe mura ba mu ke so ayi ba a’a a taimaka talaka ya kori talauci, ku tuna ba sayenmu ko ka yi ba ko ɗauki ɗora zabarku muka yi don ra’ayi, hannun da ya dangwala maku ranar zaɓe shirye yake ya dangwala ma waninku fa.

Ɗan Malisar Tarayya mun ji kana watsa ‘yar tsaba wacce ko darajar kuɗin da yaranka suke shan Askirin ba su kai ba, bayan kuwa mun san ƙarfin samunka, nan ga ba da hotunan za mu haɗa rubutun, saboda abokanku na birni su ga yanda garuruwanku suke cikin halin ha’ ula’ i, kai kuma Baba Dattijo zaku zo neman ƙuri’unmu sannan zaku gane kan ungulu ya waye, da ɗan maganin da kuke tarfawa mararsa lafiya ai gara a basu jari yafi tunda dama ciwon kun san silarsa yunwa ce da wahala, Kantoma muna saka ido mu ga da me ka zo ku kai kuma, har yanzu dai shiru.

Shin idan idanunmu suka buɗe mu ka yi fito na fito daku, ta ya ya za ku kama ma shi kansa Mai girma Gwamna da Shugaban Ƙasa wurin kawo kujerun mata, Baba waɗan nan wanda suke maka farfaganda su ne Kurfi, idan sun samu aljihunsu suke zubawa su yi Abuja idan suka ga ɗan garinsu na neman taimako su kira shi da ɗan mallaka, ba su da ƙima ko kwarjini a wurin ‘yan uwansu bare kuma’ yan gari, zasu fuskanci babban ƙalu bale ranar a fito, saboda Kurfi siyasar kishi muke yi ba ta sabo ko neman kuɗi ba, tsaf miji da mata da yaransu kowa zai zaɓi ra’ayinsa, ya ya zaku yi idan mata suka ƙi fitowa su zaɓe ku ko mu saɓi alluna domin zanga-zanga dan duniya ta fuskanci halin matsi da mu ke ciki, duk wacce mijinta ya rasu gidanta ya rushe yaranta sun shiga garari, mata babu sana’a, ga zafin talauci da wahala da yara, idan an sako mace maza ku korata gida da yaranta ga talauci ga yunwa ga babu sana’a, ba mu da jam’iyya ba mu da gwani sai wanda ya rungume mu ya tallafemu, kar ku manta kunce, “mun fi maza yawa” wannan yawan zai mana amfani wurin kayar da ku ko taimakonku, ku tsumaye rubuta na duk sati a Jarida ɗauke da hotuna. Gyara mu ke nema da ‘yancinmu ba rigima ba. Kar ku manta MATA MUNE ƘASHIN BAYAN AL’UMMA.

Fadila H Aliyu Kurfi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here