Hon Salisu Hamza Rimaye Ya Sha Alawashi Sauya Fasalin Siyasar Nijeriya

0

Tun Bayan da aka kada kugen siyasa, masu neman takara suka bazama shirya taruka na yadda za su samu hanyar lashe zaben fitar da gwani.

Gidauniyar Maigemu karkashin jagorancin Hon Salisu Hamza Rimaye Danmajalissa mai wakiltar Karamar hukumar Kankiya a Bihar Katsina su ka shirya wani gangami ga fitattun matasa wadanda suka kware a bangar siyasa, in da suka yi shirya masu bita ta musamman kan illar bangar siyasa da kuma shaye-shaye.

A lokacin da ya ke jawabi shugaban Cibiyar Hon Salisu Hamza Rimaye, ya yi kira ga matasa da su guji bangar siyasa, ya kuma bayyana masu cewa in dai saboda shi suke bangar siyasa to su bari shi gurinshi ya taimaki rayuwarsu ya sama masu madogara mai kyau wadda zai yi alfahari da su.

Ya bayyana masu cewa a baya ya dauko da shirin taimaka masu da jari da kuma sama masu horo a na noma da kiwon kiwo a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, amma sai da yawan su suka ki amfani da damar suka rika watsar da jarin da aka ba su.

Ya bayyana masu cewa Gidauniyar Maigemo ta tara su ne a nan domin ta yi masu albishir da sabon tsarin da ta shirya na taimakonsu, ta yadda zata budewa matasan fayal da hotunansu da kuma kwafi na katin zaben kowa a ciki, a duk wata zasu rika ware wasu suna basu jari ko koyar da su sana’a amma a bisa sharadin in sun shiryu sun bar munanan halaye na banga da shaye-shaye.

See also  An bayyana rasuwan malami Aliyu 'yandoto a matsayin babban rashi ga al'umar jihar Zamfara

Ya kara da cewa basu bukatar matasan suna hana abokanan adawarsu na siyasa sukar su ko kuma ce masu one term, su dai kawai suna so matasan su San ciwon kansu kuma su dogara da kansu.

Daga karshe an bayar da dama ga matasan da su tofa albarkacin bakinsu kan wannan abu da ake tsara masu. In da da yawan su suka nuna na’am da wannan tsari kuma suka yi alkwarin gyaruwa tare da yin godiya ga Shugaban wannan gidauniya ta Maigemu bisa kauna da ya nuna masu.

Matasa sama da Dari biyu ne suka halarci wannan gangami da akayi a Kofa haka kuma an bayar da tallafi ga daruruwan matasan nan take.

Gidauniyar Maigemu dai gidauniyace da aka kirkira domin tallafawa mutanen al’ummar Karamar hukumar Kankiya, wasu daga cikin ayyukanta sun bada da:

Bayar da kayan abinci da na dunkunan Sallah ga marayu.

Samar da gurabun Karatu da tallafi ga Dalibai

Daukar nauyin marasa lafiya da basu magani kyauta

Horas da matasa sama da dubu biyu ilimin na’ura mai kwakwalwa.

Daukar nauyin al’amurran addini da suka shafi wa’azi da makamantansu a kafafen sadarwa da zahiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here