Shata Masoyin Annabi ne, Don Haka Nima Ina son sa.. Shehu Dahiru Bauchi

0

Shata Masoyin Annabi ne, Don Haka Nima Ina son sa.. Shehu Dahiru Bauchi

Daga Abdurrahman Aliyu

A ranar 3 da Hudu ga wannan watan ne aka gudanar da taron kasa da kasa na tunawa da Marigayi Dakta Mamman Shata a Jami’ar Bayero da ke Kano.

A wajen taron an baje kolin fasaha daga masana da dama, kuma an samu mahalartar taron kama tun daga Malaman jami’a da ma’aikata gwamanti da yan Kasuwa da dama na ciki da wajen kasar nan.

Daga cikin wadanda suka yi jawabai a wajen taron hadda shahararren Malamin nan Shehu Dahiru Bauchi wanda ya aiko da bayaninsa ta wayar sadarwa da aka kira Malamin, in da ya bayyana cewa,

“Shata wata Babbar Jikka ce baka katuwa baka wadda in an bude ya za a ga abubuwan da aka sani da wanda ba’a sani ba, domin tarkace ne gasu nan kala-kala.

Haka kuma akwai daurin Sululu kan gwal a cikin jakar, ya Kara da cewa Shata wani masoyin Annabi ne, domin wakarsa ta Na tsaya ga Annabi Muhammadu SAW, ya bayyana cewa dukkan Annabawa da Waliyya da salihan bayin da aka taba yi a duniya duk nan suka tsaya ga Annabi Muhammadu S.A.W.

Ya bayyana cewa akwai wata boyayyar soyayya tsakanin Shata da Annabi, domin duk hidimar bikin shirya Mauludin Annabi Muhammad da ake yi a Daura to su Shata ke shirya shi, saboda haka Shata masoyin Annabi Muhammadu ne.

Shehin Malamin ya bayyana cewa Shata abokin wani abokinsa ne mai suna Alhaji Sani Auwalu wanda ya ke dan Kano ne amma yana rayuwa tsakanin Legas da Ibadan, kuma a wajensa ne da Shata zai karbi Darikar Tijjaniya, amma sai Allah ya yi masa rasuwa, daga baya na hadu da Shata inda ya bukaci da ya karbi Darikar Tijjaniya a hannunsa tun da abokinsa da zai karba a hannunsa ya rasu, amma sai ya ce mai zai zo har Bauchi ya karba, har zuwa lokacin da Allah ya dauki ransa.

Babban Malamin ya bayyana cewa in dai mutum na son Annabi Muhammadu SAW to duk abin da zai aikata Allah zai masa gafara.

Ya kara da cewa a baya Shata ke shan giya yana cewa ” Asha ruwa ba Laifi ba ne” to duk wannan ya gushe saboda Shata na son Annabi Muhammadu SAW.

Ya bayyana cewa da mutum zai tara ibadu da ayyukan alheri da yawa amma a cikin zuciyarsa baya son Annabi to in ya je Lahira Allah ba zai kalle shi ba, saboda baya son kayan Allah wato Annabi Muhammadu SAW.

Ya kara da cewa akwai wata waka ta Shata da ya ke cewa, “Don Sallah da Salatin Fatihi Dan Allah mata Ku yi aure” ya nuna cewa wannan wakar ta nuna Shata ya san girman Sallah kuma bai lalata ta ba ya ce Siyasa tafi Sallah.

Ya cigaba da cewa akwai wata wakarsa da ya ke cewa “in mutum ya girma ya san ya girma ya karbi wuridin Tijjani”, ya ce ba zai iya kawo baitin ba, amma dai wannan ya nuna cewa Shata mai son Annabi ne saboda haka yana sonsa.

Malamin ya nuna cewa yaji dadin wannan taro kuma da angaya ma shi da wuri da yazo wajen taron.

An masa tambaya kan cewa ana yin wani bayani wanda akace dhi shehin malamin shi ya aikawa Shata cewar ya ji wakar Jika amma bai ji ta kaka ba, wanda ana ganin wannan shi ne asalin wakar nan ta “Na tsaya ga Annabi Muhammadu”.

Shehin malamin ya amsa da cewa ko ma dai ba haka bane to haka ne domin Shata Masoyin Annabi ne.

Daga karshe Shehin Malamin ya yi bayanin cewa duk wani masoyin Annabi to masoyinsa ne inda ya kulle jawabinsa da cewa Shata har ya mutu bai samu ya karbi Darikar Tijjaniya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here