IYAYEN YARA SUN YI WA WANI MALAMIN FIRAMARE CAA! DON YA BAIWA ‘YA’YANSU JINGAR KIRGA SHINKAFA MILIYAN DARI.
Iyayen yaran ‘yan aji hudu a wata makarantar firamare a kasar Cana sun yi matukar cika da mamaki bayan malamin yaran nasu ya rubuta musu jinga (aikin gida). Inda ya ba wa yaran kwanaki 2 kacal su kirga masa shinkafa guda miliyan dari. Kuma yana fatan iyayen za su taimaka wa ‘yayansu wajen kidayar. Malamin ya rubuta musu jingar ne a guruf din da yake ganawa da daliban na shafin sada zumunta na WeChat.
Wannan ya jawo masa martani da dama daga iyaye yara. Inda wasu suke ganin sam aikin ba zai yiwu a kwanaki biyun da ya ce ba. Zai iya daukar shekara ma ba a gama ba. Wasu iyayen ma gani suke yi ta yaya za su ajje shinkafar da kai yawan haka a gidajensu? Iyaye sun yi ta yayata wannan aiki a shafukan yanar gizo. Domin wannan abin mamaki ne saboda gwamnatin garin tana yin hani a kan loda wa daliban firamare aikin gida mai wuya saboda a rage wa daliban wahala. Manyan dalibai ma ta yi hani da a ba su aikin da za su dauki fiye da awa daya ba su kammala ba.
Shi kuma malamin ya yi bayanin kare kansa. Inda ya ce, shi fa ba a fahimce shi ba ne. Ya ba da aikin ne domin daliban su yi amfani da kwakwalwarsu. Ba wai yana nufin su yi ta kidaya shinkafa dai-dai ba ne. Nufinsa su kirga kamar 1,000 sai su kara kamarta sau adadin da zai ba da Jimillar 100, 000,000.