JAMI’AN KWASTAN SUN SAKE KAMA KAYAN SOJOJI
Daga Datti Assalafiy
Daga garin Owerri jihar Imo jami’an tsaron Kwaston masu sintiri sun samu nasaran kama wata babbar motar daukan kaya wanda aka boye haramtattun kayan sojoji da aka shigo dasu daga Kasar waje zuwa Nijeriya.
![]()
Kamar yadda babban jami’in Kwastom na garin Owerri Mr Kayode Olusemeri ya bayyana wa manema labarai, ya ce an kama mutum biyu amma an boye sunan wanda ya yi safarar kayan haramtattun sojojin.
Wannan dai shine kusan karo na uku ko hudu da ake safaran haramtattun kayan sojoji da kasar waje a ‘dan tsakanin lokacin nan jami’an Kwastom suna kamawa, wannan fa iya wanda aka kama ne ba’asan adadin wanda aka samu nasaran wucewa dasu ba
Wannan dabi’a na shigo da kayan sojoji da wasu sukeyi abin tsoro ne kuma abin takaici.
Allah Ka tsare ‘yan Nijeriya daga fadawa hannun sojojin bogi
Allah Ka tona asirin wadanda basa kaunar Nigeria ta zauna lafiya Amin