WANI ABOKINA YA KOYA MIN YADDA ZAN YI KUKAN KARYA IDAN NA JE SAYEN FOM DI TAKARA- Sanata Shehu Sani.

0

WANI ABOKINA YA KOYA MIN YADDA ZAN YI KUKAN KARYA IDAN NA JE SAYEN FOM DI TAKARA- Sanata Shehu Sani.

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana wasu
dabaru da abokinsa dan siyasa ya koya masa ya yi idan ya je sayen fom din takarar sanata da yake son sake tsayawa a shekarar 2019. Sanatan zai tsaya ne a karkashin jam’iyyar APC. Kamar yadda jaridar ‘Herald’ ta ruwaito.

Da farko Sanatan ya bayyana yadda wasu gungun matasa wadanda suke yin fadi- tashi don tallafa wa rayuwarsu sun zo wajensa don neman izinin za su saya masa fom din takara don ya ci gaba da kokarin da yake musu a majalisar dattijai. Sanatan ya ce ya ba matasan hakuri ya ce kada su saya. Domin ba zai shiga sahun sauran mayaudaran ‘yan siyasa ba. Idan mai karatu zai iya tunawa, a kwanakin nan wasu kungiyoyin matasa sun sayi fom din takara ga gwamnan jahar kaduna Malam Nasir El- Rufa’i da kuma shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari.

Shehu Sani ya kara da cewa, lokacin da ya je sayen fom din takara, wani abokinsa dan siyasa ya ba shi hankici wanda aka barbada wa garin barkono domin ya dinga goge fuskarsa saboda a zaci kuka yake don tausaya wa al’umma halin matsin rayuwa da suke ciki. Sanata ya karkare da cewa; ” Ni kuma sai na ce masa, ni fa dan gwagwarmaya ne ba dan wasan kwaikwayo ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here