SANATA ABU IBRAHIM..BA ZAI KARA TAKARA BA!!! KO WA? ZAI MARAWA BAYA?

0

SANATA ABU IBRAHIM..BA ZAI KARA TAKARA BA!!!
KO WA? ZAI MARAWA BAYA?
Daga wakilan Taskar labarai
Binciken da jaridar Taskar labarai tayi ta tabbatar cewa Sanata Abu ibrahim..Wanda ke rike da siyasar APC ta yankin Funtua gam ..ya yanke shawarar ba zai tsaya takarar Sanata ba, a zabe Mai zuwa na 2019.binciken Taskar labarai ta tabbatar da Sanatan ya Rika Ido wake Ido bado.inda ya har ta kai ga wasu masoyan sa sun sayi Masa fom tun Yana kasar ingila.
Amma yanzu sanatan ya ji ra ayin wasu daga cikin iyalanshi da suke neman ya ajiye duk wani mukamin siyasa ya huta..ya Zama dattijo Mai bada shawarwari.
Majiyarmu ta tabbatar Mana cewa sanatan fada wa na kusa dashi cewa .takarar Sanatan yankin Funtua ya janye.ana sa ran cikin satin nan da ake ciki zai shaida wa gwamnan Katsina a hukumance. Matsayin shi.na fasa takara.daga nan. Zai shaida wa jam iyyar shi a hukumance cewa ..baya cikin Yan takarar Sanata na 2019.
Majiyarmu tace .ganawarsa da likitocin sa..zai Kama sati Mai kamawa ne..watau karshen watan satumba..Wanda zai tafi landan yayi zamansa ya huta kuma ya Rika samun kulawar kwararrun likitocin sa.dake ingila
A yanayin da ake ciki Taskar labarai ta tabbatar cewa duk Wanda magoya Bayan Abu Ibrahim na siyasa suka marawa baya..shine zai canye zaben fitar da takarar Sanata da ma wasu Yan majalisun tarayya..na yankin na Funtua. Saboda karfinsa da tasirinsa a tsakanin deliget na yankin.
A Sanata ..yanzu Haka mutane Tara suka fito neman kujerar a APC cikinsu..akwai Alhaji Bello mandiya. Daga Malumfashi shugaban ma aikatan gidan gwamnatin katsina.da farouk jobe.mai ba gwamnan Katsina shawara a harkokin bankuna daga kankara.sai janar maharazu tsiga .daga Danja. Sai nura Khalil daga Bakori.
A Yan majalisun tarayya kuma .sama da mutane hamsin ke nema a yankin Funtua.. tsakanin musawa Matazu kawai mutane Tara ke nema a APC
A jadawalin APC zasu fara tantance Yan takarar majalisar tarayya daga gobe a Abuja
Wata majiya tace a ganawar da Abu ibrahim zai Yi da gwamnan katsina.akwai yiyuwar ayi yarjejeniya…ta ya bayyana bukatarsa ..shi kuma ya ba .yaransa umurnin.su marawa Wanda gwamnati ke so baya….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here