DAN A DAWA A CIKIN JAM’IYYAR APC MAFI HATSARI A KATSINA!!!!
.….Ko za a iya maganinsa…..?
Daga wakilan Taskar labarai
Wani binciken da
wakilan Taskar labarai suka yi a siyasar jihar Katsina sun gano babu dan adawa daya tilo da yafi kowane dan adawa hatsari kamar Abubakar Samaila Isa Funtua
Matashin hamshakin attaijirin nan da ya fito daga garin Funtua yankin karadua a jihar Katsina, ya dade yana siyasa da takara a jam’iyyun adawa a lokacin da PDP na bisa karagar mulki a tarayya da jihar Katsina.
Alhaji sama’ila Isa Funtua suruki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shi ne ke daukar nauyin bangaren APC Mai suna akida a jihar ta Katsina.
Ya sayi fom na takarar gwamna duk da kuwa shugabanin APC na jiha sun shelanta cewa a takarar gwamna, gwamna mai ci Alhaji Aminu Bello Masari shi ne jam’iyyar za ta marawa baya Don ya kara wasu shekaru guda hudu.
Abubakar Sama’ila shi ne ya biyawa duk wani dan takara da yake bangarensa kudin fom, sanatoci uku ‘yan majalisun tarayya goma sha uku da kuma ‘yan majalisar jiha talatin da hudu kudin yawan su ya kai miliyoyin nairori.
Ya biya masu hatta abin da da ake biya na hakkin jam’iyya, banda kudaden fom
Ance harda dan abin sakawa Aljifu. Don kar kaga dimbin kudi sun wuce ta gabanka baka samu komai ba.
Abubakar shi ne yanzu haka akejin yake daukar nauyin wani yakin sunkuru da akewa gwamnatin Katsina ta kafofin watsa labarai da jaridu da tashoshin labarai dake a jihar.
Yanzu haka wanda ke a cikin Katsina zai rika jin sanarwa da daukar shirye shirye wanda wasu tashar Rediyo kan watsa, kuma daga karshe kaji ance sako daga kwamitin yakin neman zaben Abubakar Sama’ila Isah Funtua.
Majiyarmu da take bibiyar harkokin sa, sun ce ya ware makudan kudi da yakira don tabbatar da Dimokaradiyya amsassa a Katsina. Wanda daga cikin matakan shi ne tsaida ‘yan takara da daukar nauyin su, da shigar da kararraki kotu.
Wanda yanzu haka bangaren sa na APC akida yana da kararraki a kotu da ya kai jam iyyar APC ta jihar da gwamnatin jihar, daga cikinsu akwai kin yarda da yadda aka zabi sabbin shugabannin jam’iyyar da a kayi a baya da kuma na kin amincewa da yin tsarin zaben wakilan jam’iyya, sai dai ayi zaben mutum bayan mutum.
Ya na da tawagar kwararru da yake aiki tare dasu .wani lauya daga yankin na Funtua shi ne ke tsara Masa yadda komai zai tafi..
yayin da wani kwararren dan jarida, wanda shi ma dan siyasa ne daga karamar hukumar dandume shi ne ke tafiyar masa da harkokin watsa labarai.
Abubakar ya zama Mai hatsari saboda yana da kudi kuma baijin tsoron kashe su, da bayar dasu bai kuma jin kyashin hayar wanda ya san cewa yana da amfani ga abin da yake son cimmawa.
Wata majiya tace baya da matsala da Masari sai dai baya jin dadin ayyukan wasu mukarraban gwamnatin na tare da shi da yadda wasu ke sarrafa shi kamar sitiyari. Ance wannan yana cikin damursa.
Binciken mu ya tabbatar mana da cewa fitowar Abubakar Sama’ila da kuma yadda yake daukar nauyin adawa a Katsina na tambayar mike tsakanin Masari da Sama’ila Isah Funtua? mahaifi ga Abubakar?
Wanda dukkaninsu sun fito daga yankin na Karadua?
Sama’ila Isa Funtua. yanzu yana cikin na kusa da shugaban kasa Buhari, wanda baya da shamaki da fadar shugaban kasa, a fadar ta shugaban kasa ake masa lakabi da kunnuwan Buhari.
Don sh ine ke jiyowa sannan ya sanar da Buhari,
Wannan ma ya sanya har wasu na ganin a fadar ta shugaban kasa akwai masu goyon Bayan abin da Abubakar Sama’ila ke yi!
Ko zai iya zama barazana mai dorewa ga gwamnatin?
Majiyarmu tace adawar ta APC akida wadda Sama’ila ke daukar nauyi iyakarta zuwa zaben fitar da ‘yan takara domin ‘yan APC ne masu kishin ba za su iya juya mata baya ba, in babban zabe yazo, amma dai lokaci ne zai kara tabbatar da hakan.