Sakamakon Gasar Rubutun Gajerun Labarai Ta Pleasant Library and Books Da Makarantar Malam Bambadiya 2018
A ranar 21/09/2018 ne aka yi bakin bayarda kyautuka ka zakarun gasar rubutu ta Peasant Library da Makarantar Malam Bambadiya, bikin ya samu halartar manayan masana a bangaren adabin wadanda suka bada da Farfesa Isha Mukhtar da Dr Abu Sabe da Dr Shamsudden Bello da Sauran many an Yan jarida irin su Malam Danjuma Katsina da gogaggun Marubuta da ga sassan kasar nan da dama.
Kafin bayar da kyaututtukan an gabatar da jawabai daga bakunan mahalarta taron kan abinda ya shafi adabi da kuma shiga gasa.
Ga jerin sunayen zakarun gasar:
1. *Kabir Yusuf Fagge* Daga Jihar Kano, Taken Labari Matalauciyar Rayuwa, ya samu kyautar N55,000.
2. *Hassana Abdullahi Hunkuyi* Daga Jihar Kaduna, Taken Labari A Sasanta, ta samu kyautar N35,000.
3. *Zakariya Haruna Danladi* Daga Jihar Kano, Taken Labari Da Sandar Hannunka, ya samu kyautar N25,000.
4. Ibrahim Babangida Suraj Daga Jihar Katsina, Taken Labari Hangen Dala, ya samu kyautar N12,500.
5. Kabiru Shu’aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Ragguwar Dabara, ya samu kyautar N12,500.
6. Fadila H. Kurfi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Rayuwar ‘Ya Mace, ta samu kyautar N12,500.
7. Na’ima Abdullahi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Zagon Kasa, ta samu kyautar N12,500.
8. Jamila Muhammad Lawal Daga Jihar Kaduna, Taken Labari Tsananin Talauci, ta samu kyautar N12,500.
9. Amina Sani Shu’aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Balaguron Talauci, ta samu kyautar N12,500.
10. Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano, Taken Labari Jamhuriyar Matalauta, ya samu kyautar N12,500.
11. Fatima Husaini Ladan Daga Jihar Katsina, Taken Labari Kowa Ya Bar Gida, ta samu kyautar N12,500.
12. Hamza Dawaki Daga Jihar Kano, Taken Labari Katantanwa, ya samu kyautar N12,500.
13. Zaharadeen Nasir Daga Jihar Kano, Taken Labari Salmakal, ya samu kyautar N12,500.
14. Usman Muhammad Alkasim Daga Jihar Katsina, Taken Labari Dangina, ya samu kyautar N12,500.
15. Abubakar Yusuf Mada Daga Jihar Zamfara, Taken Labari Sauyin Rayuwa, ya samu kyautar N12,500.
Bayana wadannan kuma da aka ba ktautuka Farfesa Malumfashi Ibrahim ya yi bayanin cewa gobe kuma 22/09/2018 za a gudanar da Kwas na bita ga wasu zababbun Marubuta goma da za su koma gida suyi rubutu domin daliban Firamare da kuma karamar sakandire kan abin da ya shafi kimiya da lissafi da kuma Ingilishi, ya tabbatar da cewa kowanensu kuma zai koma gida da Naira Dubu 30 domin ya je ya wasa alkalaminsa.
An tashi taron dai da misalin karfe shidda na marece.