Farfesa Adewale Zai Gabatar Da Inogaral Lacca A Jami’ar Karatu Daga Gida
A Ranar Laraba ne za a gabatar da Inogaral Lecca karo na goma 12 a babbar hedikwatar jam’ar Karatu daga gida da ke Abuja.
Shugaban sashen addinai na Jami’ar ne zai gudanar da ita Farfesa Olubiyi Adeniyi.
A lokacin da shugaban tsangayar matakin gaba da digiri ke jawabi Dakta Mande Sama’ila ya bayyana cewa jigon da za a gabatar da Lecca a kansa shi ne Akan abin da ya shafi Addinin Kirstanci ne a Afrika.
Laccar dai zata gudanan ne da rana a babbar hedikwata Jami’ar da ke Jabi a Abuja.
Wanda zai gabatar da wannan lacca dai kwararre ne a bangarensa kuma gogge a fagen gabatar da lacca.
An haifi Farfesa Adewale a Jihar Oyo a shekarar 1963, in da yayi digirinsa na farko a a Sashen Ingilishi a Jami’ar Ile-Ife a shekarar 1984.
Ya samu horo na Tauhidin Kiristanci a makarantar Baptisma da ke Ogomosho, wanda ya kammala digirin sa akan ilimin sanin Allah, a Shekarar 1990.
Ya samu babbar Diploma a fannin aikin Jarida a makarantar Kimiya da Fasaha da ke Ibadan, sannan ya yi karatun Digiri na uku kan abinda ya shafi ilimin Littafin Injila a Jami’ar Ambros Alli da ke Ekpoma a shekarar 2005.
Ya yi shekara Biyar yana koyar wa a Jami’ar Benson Idahosa da ke Benin City.
Ya koma aiki a Jami’ar Karatu daga gida a shekarar 2006 in da ya zama Farfesa Shekara goma sha daya da ta wuce.
A Jami’ar karatu daga gida Farfesa Adewale ya rike mukamai da dama da suka hada da Shugabam cibiyar Jami’ar da ke Legas.
Memba ne shi a kungiyoyin da suka shafi malaman jami’a na ciki da wajen kasar nan, sannan ya rubuta litattafai da dama.
Shugaban Jami’ar Karatu daga Gida Farfesa Abdalla Uba Adamu shi ne, Babban mai masaukin baki a wajen taron.
Sanarwa daga Darkta Yada Labarai na Jami’ar Malam Ibrahim Sheme.