YADDA TA KAYA TSAKANIN TAKAI DA KWANKWASO

0

YADDA TA KAYA TSAKANIN TAKAI DA KWANKWASO

Yasir Ramadan Gwale

Tun muna hanyar zuwa Kaduna wajen tantance ‘Yan takara, Sanata Kwankwaso yake waya da Malam Salihu Sagir Takai akan kada yaje a tantance shi domin shiga takarar Gwamna a PDP. A saboda haka Takai ya bayyanawa Sanata cikakken batu dangane da takararsa, duk irin jawaban da Takai ya yiwa Sanata Kwankwaso a game da wannan takara Kwankwaso bai gamsu ba.

A saboda Haka Kwankwaso ya bukaci lallai da zarar Takai ya shigo garin Kaduna kar ya zarce ko Ina sai gidansa. Bayan kwarya kwaryar neman shawarwari da Malam Salihu yayi lokacin da muka tsaya yin Sallah, sai aka ce ya fara zuwa ofishin jam’iyya inda ake tantancewa, ya rubuta sunansa a cikin rejistar da aka ware don haka. Alabasshi yaje gidan Kwankwaso ya dawo.

Haka kuwa aka yi, Bayan Takai ya Isa Kaduna ya je ofishin jam’iyya ya shigar da sunansa da kuma takardunsa, sannan ya bar Faruku Iya DG na kamfen dinsa a wajen domin ya tsaya a madadinsa kafin a zo kansa, shi kuma zai je gidan Kwankwaso domin jin yadda zata kaya.

Da zuwan Malam Salihu gidan Sanata Kwankwaso ba wani bata lokaci aka shiga tattaunawa tsakaninsa da Kwankwaso kan batun takarar Gwamna. A yayin zamansu, Kwankwaso ya roki Takai akan kada ya shiga takarar Gwamna ya daure ya karbi kujerar Sanatan Kano ta kudu.

Takai ya shaidawa Sanata Kwankwaso cewar shi fa takarar nan ba shi ne ya fito da kansa ba, jema’a ne suka nuna sha’awar yayi takara, tun bai gamsu ba har ya yadda ya shiga cikin abin. Ya kewaya kananan hukumomi 44 ya zauna ya tattauna da shugabannin jam’iyya na wadannan kananan hukumomi, sannan ya kafa kwamitoci, ana aiki ba dare babu rana akansa ba tare da ya baiwa kowa ko kwabo ba, mutane ne suke tayashi wannan al’amari da kudinsu.

Haka aka shiga wannan kwaramniya har uwar jam’iyya ta kasa ta shelanta fara sayar da takardun cikewa dan shiga zabe, kuma aka je Abuja aka sayi wadannan tardun aka cike aka mayar da su. To kwatsam kuma yanzu sai nace na yi watsi da wadancan abubuwa na karbi takarar Sanata! A cewar Malam Salihu ga Kwankwaso.

Daga nan ya nunawa Sanata Kwankwaso cewar idan nayi haka ai ban kyautawa wadan da suke kashe kudi da lokacinsu akan takarar ba. Takai ya cigaba da shaidawa Sanata cewar, yanzu mutanan da suke Kano ta tsakiya da wadan da suke Kano ta Arewa suka dage sai na fito takara, suna kashe kudinsu, sannan kawai yanzu nace na karbi Sanatan Kano ta kudu, shi kenan sun sha wahalar banza a kaina. Idan nayi haka ai na nuna dan kaina nake yi ba dan Jama’a ba. Inji Takai.

Duk da wannan jawabi Sanata Kwankwaso bai gamsu ba, ya shaidawa Malam Salisu cewar “Look Malam Takai, kujerar Sanata fa Babba kujera ce, galibi sai wanda suka yi Gwamna sau biyu sune suke zama sanatoci, amma gashi yanzu kai kayi sa’a zaka shiga cikin former governors” A cewar Sanata Kwankwaso.

Sannan ya cigaba da cewa Takai ni fa aka baiwa 51% na jam’iyyar nan. Takai yace, Distinguish bama musu cewa kai ne jagoran PDP a Kano, mun yadda, mun gamsu. Amma abinda nake gani kawai shi ne ka zabi wanda duk kake so yayi takarar nan mu shiga zaben fidda Gwani idan mun yi Nasara shi kenan, idan kuma kayi Nasara akanmu shi kenan. Sanata Kwankwaso yace bana son Mu shiga zaben fitar da gwani.

See also  Mutane 20 sun kone ƙurmus a haɗarin mota a Oyo

Ana tsaka da wannan tattaunawa tsakanin Takai da Kwankwaso, can kuma a ofishin jam’iyya layi yazo kan Takai, dan haka, Farouk Iya yake ta yiwa Malam Salihu waya lallai ya katse wannan tattaunawar yazo a tantance shi. Haka dai, dole, Takai ya katse wannan tattaunawa da Sanata Kwankwaso ya dawo ofishin jam’iyya aka kuma duba takardunsa aka tantance shi aka bashi satifiket na shaidar cewar yazo an tace shi.

Duk da anyi Haka Kwankwaso bai gamsu ba. Ya sake yiwa Takai waya akan yazo a cigaba da tattaunawa ko zasu Iya shawo kansa ya hakura ya karbi tayin kujerar Sanata. Karshe dai Malam Salihu yayiwa Kwankwaso kankat, inda ya ce masa, ko zasu shekara suna tattaunawa ba zai sauya daga abinda shi da jama’a suka yi matsaya akansa ba. Abinda kawai yake fata shi ne, a shiga zaben fidda Gwani, tunda Akwai Ibrahim Little da Jafar Bello Sani da Sadiq Aminu Wali duk an tantance su kawai a yi zaben fidda gwani.

Jin hakan ta sanya Sanata Kwankwaso ya saduda, ya gamsu cewar Takai ba zai karbi wannan tayin nasa ba. Da farko dai Kwankwaso yayi zaton Takai tubus tubus ne, daga an zauna an daddana shi da maganganu zai karbi duk tayin da akai masa. Amma Ina, Takai ya nuna jajircewa da tsayawa kyam akan abinda ake kai.

Bayan Takai ya dawo wajen tantancewa aka kuma tantance shi Daga nan ya cigaba da tattaunawa da Kwankwaso kan ya hakura a yi zaben fidda gwani da wanda yake so din, idan yaso wanda Allah ya baiwa nasara shi kenan.

Karshe dai da Kwankwaso ya gaza samun abinda yake so a wajen Takai dan haka, ya fito da nasa dan takarar Kabir Abba Yusuf. Dan haka, ba mu da wani tararrabi ko fargaba kan zaben fidda gwani, zamu shiga zaben fitar da gwanin da za ai a Kano mako mai zuwa In sha Allah. Kuma ga Allah muka dogara shi ne mai yi ba wani mahaluki ba, idan yace Malam Salihu Sagir Takai zai yi to babu wani mahaluki da zai Iya tarewa ko ya hana. Allah shi ne abin dogaronmu, mun kyautata zato gareshi.

Wannan jajircewa da dagewa da Malam Salisu Sagir Takai ya nuna ya sanya na yadda na kuma sake gamsuwa da shi a matsayin Jagora na gari, wanda in sha Allah ba zamu taba yin da-nasani kan Binsa ba. Muna adduar Allah ya shige masa gaba yayi masa jagoranci ya dora shi akan daidai. Ko da mulki ko babu mulki Malam Salihu Sagir Takai na yadda na gamsu na baka mubayi’ata. Allah shi ne zai bamu.

Yasir Ramadan Gwale
23-09-2018

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here