FITO DA LADO TAKARA; yadda Jami in zabe ya kasa fadin yawan kuri u…da masu kuri ar

0

FITO DA LADO TAKARA; yadda Jami in zabe ya kasa fadin yawan kuri u…da masu kuri ar

Daga Danjuma Katsina

A Ranar litinin​ da ta gabata.jam iyyar PDP ta shelanta sunan yakubu lado Dan marke. a matsayin Dan takarar da zai tsaya Mata a Inuwar jam iyyar a takarar gwamnan Katsina..
Wanda ya shelanta matsayin shine Alhaji Sani Abu minista Daya daga. Cikin dattawan jam iyyar..ya bayyanawa manema labarai cewa..Yan takarar sunyi kokarin ganin cewa sun cimma matsayar a tarurrukan da sukayi a kaduna abin yaci tura..sai aka fito da tsari na cewa a gayyato shugaban nin jam iyya na kananan hukumomi da wasu masu ruwa da tsaki a hadu a ofishin jam iyyar na jaha..a fitar da Dan Takara guda Daya
Sani Abu minista yace da aka Hadu shine akayi zabe Wanda duk Yan takarar suna a wajen .bada mutum Daya shine Ahmad Aminu
Sani Abu minista yace da aka kammala zaben .sai yakubu lado yayi nasara..A wajen manema labarai sukayi sukayi .ya fada masu yawan wadanda suka jefe kuri ar ..da yawan kuri un da kowa ya samu Amma yaki..Yana cewa ..ya !manta sai ya Tambaya .in an shaida Masa.
Don haka daga bakinsa ..ya kasa. Fada..Amma nan take shugaban jam iyyar Alhaji Salisu majigiri​ ..cewa yayi ga takardar nan da yawan masu kuri a da abin da kowa ya samu Amma ba dai dai bane a bayyana.
Sai dai binciken da mukayi mun gano cewa .da akayi kuri ar ..Sanata yakubu lado Dan marke..ya samu kuri u.hamsin da shidda(56) barista Abdullahi faskari ya samu kuri u Sha shidda (16) Alhaji umar Abdullahi tata kuri u hudu(4) Ahmad kofa kuri u hudu (4) sada ilu kuri u hudu (4) Musa nashuni kuri u biyu (2) Ahmad Aminu kuri a Daya (1)
Binciken mu ya tabbatar Mana cewa Yakubu lado shine Dan takarar da tsohon gwamnan Katsina..barista ibrahim shema..ke marawa baya..Wanda kuma har yayi magana da wasu Akan hakan..
Inda ya shaida masu cewa..ana son Wanda zai tsaya​ ya Zama Mai kudin da zai iya takara..Wanda kuma Yakubu lado shi ke da Wannan kudin..
Anyi zargin cewa anyi amfani da kudi wajen Jan ra ayin wadanda suka yi zaben! Zargin da Sani Abu minista ya karyata a wajen taron na manema labarai…yace bai da masaniyar amfani da kudi.
Shidai Yakubu lado Dan asalin Kankara ne daga Garin Dan marke.amma yanzu Yana zaune ne a Kano .Inda ya kwashe kowa nasa da jahar Katsina .ya mayar dasu Kano da Zama .
Sai dai in lokacin siyasa tayi ya shigo Katsina yayi siyasa da an Gama ya koma.ya taba shugaban karamar hukumar kankara.wanda a lokacin ya fuskanci zanga zanga kala ..a Bisa matsaloli mabambanta a karamar hukumar…an taba zargin sa da takardun bogi na wata kwaleji… zargin da ba ida kammala​ tabbatar wa ba..
Yakubu​ lado Dan siyasa ne da ke da CeCe kuce masu yawa tare dashi..
Binciken da mukayi ..zaben sa da PDP tayi ya jefa Yan jam iyyar cikin wani yanayi na jimami.takaici da Bakin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here