KO KOTU ZATA TSAIDA ZABEN FITAR DA DAN TAKARAR GWAMNA NA APC A KATSINA?

0

KO KOTU ZATA TSAIDA ZABEN FITAR DA DAN TAKARAR GWAMNA NA APC A KATSINA?
Daga wakilan Taskar labarai
Wata majiya dake tattare da Dan takarar gwamnan Katsina na APC bangaren akida … Alhaji Abubakar ismaila Isa Funtua..sun shaida Ma Taskar labarai cewa tsakanin​ yau laraba 26/9/2018 zuwa jumma a. 28/9/2018 lauyoyin bangaren, sun dage Don ganin cewa .sun samo umurnin kotu na a tsaida zaben da za ayi na fitar wa da APC Dan takarar gwamna.a ranar 29/9/2018.
Bangaren na Abubakar sama ila, sun shigar da Kara kotun ne .akan cewa deliget da zasu yi zaben .Basu cancanta ba.don ba a zabe su ba a hanyar data Dace.kuma ba abi ka ida ba a wajen fito dasu daga mazabu ba..
Akan Haka bangaren nasu suka bukaci a yi zaben gwamna na Kato Bayan kato.abinda da jam iya a jaha da masu ruwa da tsaki suka ki amincewa. Kuma a jiya APC ta kasa ta fitar da sanarwar jaha Katsina na cikin jihohin da zasu yi zabe ta hanyar deliget..
Akan Haka ne bangaren akida a APC suka tafi kotu suna neman a tsaida zaben na Katsina har sai an saurari bukatar su..ta cewa deliget na Katsina ba ingattattu bane.
Majiyar Taskar labarai tace wasu manyan lauyoyi suka shigar da karar a wata kotun abuja.kuma yau ..laraba zata zauna .ta fara sauraren bukatar na APC bangaren akida ta Abubakar samaila​ Isa.
Wakilan Taskar labarai zasu kasance a kotun duk yadda ta Kaya zaku a a yau..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here