AN CABKE WANDA KE BARAZANA GA TSOHON MATAIMAKIN SHUGABAN KASA KUMA MAI NEMAN TAKARAR SHUGABAN KASA ATTIKU ABUBAKAR

0
669

AN CABKE WANDA KE BARAZANA GA TSOHON MATAIMAKIN SHUGABAN KASA KUMA MAI NEMAN TAKARAR SHUGABAN KASA ATTIKU ABUBAKAR

Daga Abdurrahman Aliyu

Hukaumar ‘yansanda Nijeriya ta kama wanda me barazana ga Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Wanda aka kama din mai suna Augustus Akpan dan shekara 43 dake kauyen Edemaya a karamar hukumar Ikoti Abasi da ke jihar Akwa Ibom. An kama shi da waya kwara daya kirar Samsung( Galaxy S6 Edge +) wadda da ita ce ake zargin yana tura sakonnin barazanar ga Tshohon mataimakin shugaban kasar da iyalinsa.

Sakunnan da aka samu sun hada da, Wanda ya turawa Tsohon mataimakin shugaban kasar kamar haka:

“Turaki Attiku muna bibiyarka da kai da iyalanka, kuma muna umurtarka da ka janye daga takarar da ka fito ta shugaban kasar, ko mu kashe ka mu kuma yi wa matarka da ‘yarka fede. Muna bibiyar Bakar Diyarka Maryam da ke aiki a CBN, zamu kamata mu yi mata fede sannan mu kasheta.

Haka kuma diyarka Fatima tsohuwar kwamishinar Lafiya ta jihar Adamawa, muna da bayanai kanta, da hotunanta da take tsirara, sannan karuwar matarka Jennifer duk muna da bayanai kansu. Saboda haka muna bukatar ka bar Buhari ya maimaita, mun san cewa kaina mafi girma a cikin duk masu neman takara a Jam’iyyar PDP, shi ya sa mu ke bukatar ka janye.

Zamu shayar da kai guba da iyalanka Idan har baka janye ba, sannan kuma sai ka fara sauraren abin da zai faru da iyalanka, kafin a so kanka. Mun San inda Yaranka Duke da kuma inda suke zuwa, mun sanya ido kan diyarka Maryam sosai a gida mai lamba 5 a Buzi da kuma mai lamba 5 a Lake Maracaibo”

Sako na biyu kuma an aika shi ne ga matar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Atiku Abubakar, kamar haka:

” Jennifer ki sanar da mijinki da ya janye daga takar neman shugabancin kasar, ko kuma muna kashe duo iyalanku, mu yi fyade a gareki da kuma dukkan ‘yayanku sannan mu kashe sauran, haka kuma muna san ofishinki a lamba 13 dake titin Danube a Maitama. Zamu mamaye wuri mu yi fyede ga dukkan Ku, amma in Baki son faruwar haka kina iya bashi shawara ya janye daga neman takarar shugaban kasa da ya ke.”

Sako na uku kuma an aika shi ga diyar Atiku Abubakar he Rukaiya, sakon ya na dauke da bayanai kamar haka:

Ki sanar da mahaifinki ya janye kudirinsa na neman takarar shugaban kasa, Idan kuma ya kiya to muna tabbatar maki zai sha mamaki, domin sai mun yi maki fyade, sannan mu kashe ki ke da diyarki. Babu wasu jami’an Yansandan da zasu iya tsayar da mu abin da muka yi niyya, mun san duk wani wuri da kike rayuwa, wanda ya hada da lamba 5 a Buzi da kuma lamba 5 a Mairacaibo. Ku jaraba mu zamu yada jininku.”

Bayan shigar da korafi daga Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Mataimakin Shugaban ‘Yansanda na kasa bangaren bincike na IRT sun kama wanda ake zargi Augustin Akpan.

An kama Augustin ne a Toliget kusa da babban titin Lagos zuwa Ibadan, karkashin tawagar kwararren Dansanda DSP Abba Kyari, a bisa hanyarsa ta tserewa daga kasar. A lokacin da ake bincikarsa ya bayyana cewa ya yi hakan he domin ya tilastawa Atiku ya bashi kudi.

Bincike ya tabbatar da cewa Augustin kwararren Dan damfara ne, sannan baya da nasaba fa wata jam’iyyar siyasa, ya ambaci a bar Buhari ya maimaita me da kuma kama sunaa sauran ‘yan takarar PDP domin kawai ya kasar da hankali mutane akansa.

Wanda ake zargin yakware a harshen Inglishi da Ibibio da Rashen da kuma Harshen Fotogist, wayar da ya yi amfani da ita da kuma layin duk mallakar wata mata me da suka yi wa fashi a watannin baya da suka wuce.

Augustin Akpan kwarare ne wajen shirya irin wannan damfarar domin ya karbi kudade na gidada na waje daga hannun many an mutane da yawa kan irin wannan salon da!fara.

Bayan an kammala bincike za a mika wanda ake zargin kotu domin a yanke masa hukuncin da ya dace da laifinsa.

Ag. DCP Jimoh Moshood,
Jami’in hudda da Jama’a na rundunar ‘yansanda ta kasa da ke Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here