APC AKIDA SUN RUBUTA TAKARDAR KOKE!!!

0

Zaben fidda gwani
APC AKIDA SUN RUBUTA TAKARDAR KOKE!!!

Daga wakilan Taskar labarai


Zaben fitar da Dan Takarar gwamna APC na jahar katsina..ya kare ya bar baya da kura..zaben Wanda ya gudana a jiya lahadi.wanda gwamnan na Katsina maici Alhaji Aminu Bello Masari ya lashe da sama da kuri u dubu biyar.
Tun kafin a fara zaben .Yan Takara guda biyu na APC Abubakar samaila Isa da Garba Sani dankane suka gabatar da wata takardun koke ga kwamitin da aka turo Don gudanar da zaben sun kuma Kira shugaban jam iyyar na kasa Mista Adam ashimolu sun Masa korafi…Inda yace su rubuto
A takardun. Kamar yadda Taskar labarai ta samu.sunyi korafin cewa Yan kwamitin an kawo su cikin dare a wani jirgi da suke zargin gwamnatin Katsina ta dau shatarsa..kuma suna isowa suka zarce cikin Daren suka gana da Jami an gwamnatin Katsina.
Yan takarar sunyi korafin cewa.ba a neme su ba sai a ranar zaben da karfe Sha biyu na Rana kuma aka shaida masu cewa..an kammala tantance masu zaben kuma zaben za a fara a koyaushe.
A takardun sun Yan takarar sun fadawa Yan kwamitin cewa akwai maganar kotu da aka shigar Akan masu zaben da ma shi kansa wannan zaben. Kuma a matsayin su na wadanda suka sayi fom uwar jam iyya ta tantance su..ta Basu damar suna iya takara ..jam iyya ta jaha Bata taba tuntubarsu ba Akan komai..sai dai suji wai wai..
A takardun sun ce . abin da kayi masu a matsayin su na Yan takarar da jam iyya ta amince dasu..ya Saba wurare da yawa na dokokin​ jam iyya..da dokar da zabe ta kasa kuma suka nemi Yan kwamitin su gaggauta gyarawa kafin lokaci ya mute masu..
Takardar​ da suka gabatar sakataren kwamitin zaben na Katsina Dakta Haruna yarima ya sama Mata Hannu..cewa ya amsa.a madadin kwamitin.
Wani Dan APC akida yazo har ofishin Taskar labarai Inda yayi zargin cewa an bubbugi mutanen su a filin taron da za a yi zaben .an fasa wa wasu motoci an kuma kama wasunsu cikin wadanda aka Kama harda Yan takarar su..na majalisar jaha da na majalisar tarayya.
Zargi da Taskar labarai Bata iya tabbatar wa ba a wajen Yan sanda..Don Jami in hudda da jama a na Yan sanda ..bai dauki waya ba da aka Kira shi
Jam in na APC akida yace.zasu dau matakan Shari a Akan wannan cin zalun da akayi masu.na bugu da bannata dukiya da Kama masu mutane da akayi.
Gobe talata..2/10/2018 za a cigaba da sauraren biyu daga cikin karrarrakin da APC akida suka shigar Akan zabubbukan na Katsina.tun daga na deliget har zuwa na shugaban nin Jami iyar jahar da kuma na zaben Yan takara da akeyi..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here