RIKICI A JAM IYYAR PDP::::
YADDA DAKTA MATAZU YA KUSA AFKAMA MUTTAQA RABE DARMA
Daga wakilan Taskar labarai
Saura Kiris da an kwafsa tsakanin Dakta shehu Garba Matazu tsohon Dan majalisar tarayya kuma tsohon Mai baiwa” gwamna shawara da injiniya Muttaqa Rabe darma tsohon kwamishina kuma tsohon shugaban ptdf a wani taron masu ruwa da tsaki na PDP da ya faru a farkon satin nan a sakatariyar jam iyyar ta PDP jahar Katsina.
ABin da ya faru shine an zo taro ne sai injiniya Muttaqa Rabe darma ya ke bada wasu shawarari masu amfani Wanda zasu taimakawa jam iyyar daga maganin fuskantar matsalolin dake gabanta na fadawa Rami gaba dubu.mai wuyar fita
Sai kawai Garba Matazu ya fara bakaken maganganu da batanci da bubbutai..Yana amfani da kalmomi na Rashin dattaku..kamar yadda Taskar labarai taji .yadda abin ya faru a waya da wani a cikin taron ya dauka.a asirce.
Muttaqa ma sai ya fara maida Masa amsa cikin natsuwa.wanda shi kuma matazu ya Rika hassala.
Daga baya aka Shiga tsakani.
Binciken Taskar labarai ya tabbatar cewa .. Gwamnatin APC sun Dade suna ZAwarcin injiniya Muttaqa Rabe darma Amma yaki Mika wuya..ko sharadi ma yaki badawa ..an ruwaito Yana cewa kamar cin Amanar marigayi umaru Musa Yaradua ne ,Bayan ransa ya bar jam iyyar PDP. Kuma duk hidimar da yayi wa PDP yaki shiga kowace takara a zaben da za ayi na 2019
Binciken mu ya tabbatar Mana Dakta shehu Garba Matazu..yayi ZAwarcin komawa APC Amma suka ki amsarsa.. jaridar Taskar labarai ta taba zurfin bincike Akan Haka Wanda a lokacin har sukayi magana ta sakon kar ta kwana .da bala Abu musawa mataimakin shugaban APC shiyyar Funtua.da kuma wasu jiga jigan PDP.
Taskar labarai sun samu magana da wasu jigagan APC a karamar hukumar matazu.suka tabbatar da cewa Dakta Matazu. na ZAwarcin. APC har ma daga gidan gwamnatin Katsina an tuntube su..me suka gani? Amma bisa wasu dalilai suka ce ..ba zasu amshe shi ba..