fitar da sanata na PDP a shiyyar Daura
DELIGET SUNYI MA SHUGABANNIN JAM IYA TAWAYE
Jiya aka fitar da Dan takarar Sanata na PDP a shiyyar Daura..wanda Alhaji Mani nasarawa yayi nasara Akan sauran yan takarar Alhaji Abdu Yan doma da Kabir Ahmad Babba.
Wani abin da ya faru kamar yadda wakilan Taskar labarai suka tabbatar shine . tawaye da deliget sukayi suka ce ba zasu zabi abin da uban jam iyya ibrahim shema ke so ba..zasu ..zabi Wanda suka ga ya cancanta ne. A wajen su.
Taskar labarai ta tabbatar cewa anje filin zaben da niyyar cewa za ayi zabe tsakani da Allah.da Jami an PDP suka lura cewa deliget wanda suke so..bashi ne uban jam iyya ibrahim shema ya wanke ba .. sai aka fara zaune zaune da kulle, da kiraye kirayen waya
Daga baya aka shaida masu Kai tsaye cewa zabin ibrahim shema shine a zabi Abdu yandoma.ai nan take deliget din , sai sukayi tawaye..suka ce basa yi kuma uban kuturu yayi kadan..
Taskar labarai ta samu tabbacin cewa shema ya Rika bugo waya yana son magana da shugabannin jam iyya Don su lallashi deliget..amma shugabannin da kuma deliget suka ki sauraren shi.
An jiyo wani na Barka zagi Yana fadin. Wasu kalamai marasa dadi akan uban jam iyyar
Da tawaye yayi tawaye dole aka tafi zabe .Inda zabin da deliget ke so shine Alhaji Mani nasarawa yayi nasara .yayin da Abdu yandoma yazo na biyu .Kabir Babba yazo na uku.
PDP Bata da matsalar takara a shiyyar Funtua Inda aka tsaida Alhaji shehu inuwa imam.sai Katsina da Alhaji Hamisu Gambo Dan lawan ya fito.